Barkanmu da warhaka manyan gobe (13)

Barkanmu da warhaka Manyan Gobe tare da fatan ana lafiya. A yau na kawo muku labarin jarumai. Labarin ya bayyana yadda jarunta ke ceton mutum. A sha karatu lafiya. Taku Amina Abdullahi. Labarin Jarumai Akwai wata ‘yar Sarki mai matukar kyau. Tsabagen kyau ko tabo babu a jikinta. Ga shi ta isa aure amma kowa […]

Barkanmu da warhaka manyan gobe (13)
Barkanmu da warhaka manyan gobe (13)

Barkanmu da warhaka Manyan Gobe tare da fatan ana lafiya. A yau na kawo muku labarin jarumai. Labarin ya bayyana yadda jarunta ke ceton mutum. A sha karatu lafiya.

Taku Amina Abdullahi.

Labarin Jarumai

Akwai wata ‘yar Sarki mai matukar kyau. Tsabagen kyau ko tabo babu a jikinta. Ga shi ta isa aure amma kowa yana tsoron zuwa wajenta zance domin inda take akwai zaki.
Rannan mahaifinta ya ce idan da mai son ‘yarsa aure ya fito kuma ya fara zuwa zance. Nan da nan samari suka fara fitowa. Da yawa daga cikinsu daga sun ji an ambato ‘zaki’ sai su tsorata su ce ba za su iya ba sun hakura.
Ana cikin hakan sai samari uku suka ce za su inda take. Saurayi na farko ya je har sun yi hira a hanyarsa ta dawowa sai zaki ya fito ya kashe shi.
Saurayi na biyu ya kama hanya bai ko isa wajen gimbiyar ba sai ga zaki ya fito. Yana kokarin ciro wuka sai zaki ya hau kansa ya kashe shi.
Saurayi na karshe ya ce gara ya dage ya tafi da kwari da baka da wuka da kuma bindiga.
ya samu dai har ya isa bai ga zaki ba. Suna cikin hira sai ga zaki ya fito nan take ya fitar da kwari da baka ya soki zaki. Zaki kuwa ya kwanta ya mutu.
Labari ya isa ga sarki. Sarki ya ce ai wannan saurayin ne ya dace da ya auri ‘yarsa domin ya fi son bai wa ‘yarsa jarumi.
Hakan aka yi aurensu.