Barkanmu da warhaka manyan gobe (14)
Barkanmu da sake kasancewa da ku a wannan filin namu na Manyan Gobe. A yau na kawo muku labarin ‘Takitse’. Labarin na koyar da illar mugunta. A sha karatu lafiya. Taku: Amina Abdullahi ‘Takitse’ Akwai wata tsohuwa wadda ba ta da karfin yin komai. Tana da sa. Wannan sa yana taya ta aikin gida .Wata […]
Barkanmu da sake kasancewa da ku a wannan filin namu na Manyan Gobe. A yau na kawo muku labarin ‘Takitse’. Labarin na koyar da illar mugunta. A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi
‘Takitse’
Akwai wata tsohuwa wadda ba ta da karfin yin komai. Tana da sa. Wannan sa yana taya ta aikin gida .Wata rana ma har aikensa take yi.
Rannan wani ya zo shan ruwa ya yi sallama a gidan tsohuwar sai sa ya amsa. Ya ce zai sha ruwa sai sa ya gaya wa tsohuwa sai tsohuwa ta kai wa bakon ruwa ya sha.
Sai labara ya isa ga Sarki. Sarki ya ce a je a dauko masa wannan sa. Tsohuwa ta ba su hakuri cewa wannan sa ne kadai take da shi amma sun ki ki ji.
Dogarai suka yi su kwance sa, suka kasa. Sai suka ce wa tsohuwa ta sa shi ya kwantu ko su kashe ta. Sai sa ya kwantu.
Suka yi kokari su tafi da sa ya ki tafiya sai da ta ce ya tafi sannan ya tafi. Haka da za a yanka shi ma ya ki yankuwa sai da tsohuwa ta umurce shi.
Sai dogarai suka ce da tsohuwa ko akwai abin da take so a cikin shanun? Ta ce tana son kitse da hanta da hanji da huhu. Sai ta tattara su ta ajiye a tukunya.
Kullum idan tsohuwa ta tafi unguwa sai ta ga an share mata gida. Rannan ta labe sai ta ga ‘yan mata hudu kyawawa. Sai ta same su ta tanbaye su sunansu. Suka ce hanji da hanta da huhu da kitse.
Rannan aka sake yin bako aka umarci kitse ta kai ruwa sai suka sace ta. Aka hada ta da kishiya. Kishiya ta dinga gallaza mata tana saka ta aiki a rana. Har ta narke. Da kyar ta dawo kamar da.
Rannan sai ta gudu gida sai ta hadu da ‘yan uwanta suka zama babban dodo. Suka je suka kashe sarki da kishiyar.