Barkanmu da warhaka manyan gobe (15)

Tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin Musa mai a daidaita sahu. Labarin ya kunshi yadda Musa ya kyautata wa wasu yara shi ma ya ribanta da su. A sha karatu lafiya.  Taku; Amina Abdullahi. Musa mai a daidaita sahu A wani gari ne ana tafka ruwan […]

Barkanmu da warhaka manyan gobe (15)
Barkanmu da warhaka manyan gobe (15)

Tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin Musa mai a daidaita sahu. Labarin ya kunshi yadda Musa ya kyautata wa wasu yara shi ma ya ribanta da su. A sha karatu lafiya. 

Taku; Amina Abdullahi.

Musa mai a daidaita sahu

A wani gari ne ana tafka ruwan sama ga shi ko ina ya jike. Saboda ruwan saman da aka yi sai garin ya yi sanyi sosai. Akwai wasu ‘yan makarantar jami’a sun sha’afa da hira. Duba agogonsu ke da wuya sai suka ga ashe dare ya yi suna son komawa gida.
Sai suka fita neman a daidaita sahu da yawa ba su tsaya musu ba illa Musa. Sai suka roke shi da ya kai su inda za su sayi shayi. Da suka isa gurin, suka yi da Musa ya sha amma ya ki. Har abin ya bai wa daya daga cikin yaran haushi.
Da suka gama shan shayinsu, sai suka ce da shi ya kai su gida. Bayan sun isa gidan ne, sai suka ga Musa bai caje su kudi da yawa ba. Abin sai ya ba su mamaki.
Sai daya daga  cikin yaran ya ce don Allah ya gaya musu dalilin da ya ki shan shayi da su. Musa ya ce ai mai dakinsa ne ta haihu kuma yana kokarin neman kudin suna. Jin hakan sai yaran suka tausaya masa suka hada masa kudi mai yawa. Amma Musa ya ki karba. Da kyar suka ci nasara ya karba. Musa ya gode musu. Ya ce ai kudin da suka ba shi ma ya ishe shi ya sayi kayan suna.