Barkanmu da warhaka manyan gobe (2)

Tare da fatan ana cikin koshin lafiya Allah Ya sa haka amin. A yau na kawo muku labarin wasu aladu uku ne. Labarin ya kunshi yadda wayo ya ceci daya daga cikin aladun. A sha karatu lafiya. Taku; Amina Abdullahi. ‘labarin karen daji da wasu aladu uku’ Akwai wani alade yana da yara uku amma […]

Barkanmu da warhaka manyan gobe (2)
Barkanmu da warhaka manyan gobe (2)

Tare da fatan ana cikin koshin lafiya Allah Ya sa haka amin. A yau na kawo muku labarin wasu aladu uku ne. Labarin ya kunshi yadda wayo ya ceci daya daga cikin aladun. A sha karatu lafiya.

Taku; Amina Abdullahi.

‘labarin karen daji da wasu aladu uku’

Akwai wani alade yana da yara uku amma ba zai iya kulawa da su ba domin mahaifiyarsu ba ta da rai don haka, sai ya ce da su kowa tasa ta ficce shi.
Ga shi kuma aladun kanana ne ba su da inda za su kwanta. Kuma akwai labarin da ke yawo a gari cewa akwai wani karen daji dake cinye dabbobi. Don haka sai suka shiga neman inda za su fake.
Wata rana sai daya daga cikin aladun ya hadu da wani mutum yana dauke da kara. Sai ya roki mutumin domin ya taimaka masa da karan yana so ya gina gida sai mutumin ya ba shi ya gina gida. Da dare ya yi sai ya ji karen daji ya yi masa sallama amma ya ki bude masa kofa. Sai Karen dajin ya rusa gidan da karfin tsiya sannan ya shiga ya cinye shi.
dayan aladen kuma ya samu katako ya yi gininsa. Duk da haka shi ma bai tsira wajen karen dajin ba shi ma karen ya cinye shi.
Sai dayan da ya rage ya roki masu gini da su bashi bulo. Haka ya gina gidansa da bulo. Ko da karen dajin ya zo, sai ya gagara shiga gidan. Karen na ta yi wa aladen da dadadan kalamai don ya bude masa kofa amma yaki bude wa.
Rannan sai karen dajin ya hango wani rami a saman kwanon aladen sai ya ce zai shigo masa ta sama idan bai bude kofar ba.
Shi ko aladen sai ya yi maza ya dora katuwar tukunya mai cike da ruwa sannan ya kunna wuta. Nan da nan ruwa ya tafasa a daidai tsakar dakin. Ko da karen daji ya fado ta sama sai cikin tukunya mai dauke da tafasassen ruwan zafi. Nan da nan alade ya mayar da murfin tukunya ya rufe. Bai bude ba sai da karen ya dafu sannan shi ma ya cinye shi.