Barkanmu da warhaka manyan gobe (3)
Sallama a gare ku Manyan gobe tare da fatan alheri. Ya ya zabe?Koda yake nasan yawanci ba ku isa zabe ba.Amma na san kun taimaka da addu’ a. A yau na kawo muku ‘Labarin shehu da dabbobinsa.’ Labarin yana nuna yadda taurin kai yake hana cin nasara .A sha karatu lafiya. Taku kaji da agwagi […]
Sallama a gare ku Manyan gobe tare da fatan alheri. Ya ya zabe?Koda yake nasan yawanci ba ku isa zabe ba.Amma na san kun taimaka da addu’ a. A yau na kawo muku ‘Labarin shehu da dabbobinsa.’ Labarin yana nuna yadda taurin kai yake hana cin nasara .A sha karatu lafiya.
Taku kaji da agwagi da dawaki da shanu da kuma awaki.
A kullum yana barinsu su fita kiwo kuma kowanne daga cikinsu sai lokacin da ya ga dama yake dawowa.
Rannan sai wani abin al’ajabi ya faru. Shehu ya ga kamar za a yi ruwan sama da kankara. Nan take ya tura direbansa ya kwaso su.
Direba ya fara zuwa wajen kaji ya ce da su “Malam Shehu ya ce na kai ku gida don akwai alaman ruwan kankara”. Sai suka yi masa dariya suka ce ba za su dawo ba. Sai direba ya kara gaba ya je wajen awaki ya ce da su “Malam Shehu ya ce ku dawo domin za a yi ruwan kankara”. Suma suka sake kwashewa da dariya “ta ya ya malam Shehu ya san cewa za a yi ruwan kankara?”
Haka dai ya rika zuwa daga wajen wannan dabbar zuwa waccan amma babu wanda ya yadda ya bi deriba gida.
Bayan ’yan mintuna kadan sai aka fara iska da ruwa can sai ga tika-tikan kankara suna fadowa. Direba ya sake tuko motarsa ya je ko yanzu za su canza shawara.
A lokacin da ya isa da yawansu ma sun mutu dabbobi biyar ne kawai suka tsira da rayukansu.