Barkanmu da warhaka manyan gobe (6)

Barkanmu da sake kasancewa da ku manyan gobe tare da fatan alheri kuma da fatan kuna nan lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Likita mara gaskiya’ labarin yana kunshe ne da yadda rashin gaskiya ya sanya aka kulle Likita a cikin firsina. A sha karatu lafiya. Taku; Amina Abdullahi Labarin wani Likita Akwai wata […]

Barkanmu da warhaka manyan gobe (6)
Barkanmu da warhaka manyan gobe (6)

Barkanmu da sake kasancewa da ku manyan gobe tare da fatan alheri kuma da fatan kuna nan lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Likita mara gaskiya’ labarin yana kunshe ne da yadda rashin gaskiya ya sanya aka kulle Likita a cikin firsina. A sha karatu lafiya. Taku; Amina Abdullahi

Labarin wani Likita

Akwai wata tsohuwar mata mai kudi sosai amma makauniy ce. Sai ta kira Likita ta ce da shi ya taimaka ya gyara mata idanunta don ta rika ganin gari. Amma akwai yarjejeniyar da ta yi da Likitan. Yarjejeniyar ita ce, ba za ta biya shi kudi ba idan bai gyara mata idonta ba. Idan kuwa ya gyara mata ido har ta fara gani, za ta ba shi kudi mai dinbin yawa.
A kullum idan Likita ya zo gidanta akwai abin da zai sata. Yau ya saci kujeru, gobe ya saci talabijin da sauransu har ya kwashe mata kayan gidanta tas. Sannan ya gyara mata ido.
Tana warkewa ta ce da shi ba za ta biya ba. Abin ya bai wa Likita haushi sai ya kai ta kara kotu.
Lauya ya ce da ita me ya sa ba za ta biya Likita kudinsa ba? Ta ce ai ba ta gani sosai saboda makanta, tana da abubuwa a gidanta, amman yanzu kuma ba ta ga ko daya ba,bayan an gyara mata ido. Sai lauya ya gane abin da take nufi,ya yi wa Alkali bayani.Sai Alkali ya ce a kama Likita a sanya shi a kurkuku har tsawon shekaru biyar.