Barkanmu da warhaka manyan gobe (7)

Tare da fatan alheri kuma da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin Ado da Bala labarin yana nuna mugunta ba tad a kyau. A sha karatu lafiya. Taku: Amina Abdullahi Labarin Ado da Bala Ado mutum ne mai tausayi da tsoron Allah. Yana da yaya Bala shi kuma mai son […]

Barkanmu da warhaka manyan gobe (7)
Barkanmu da warhaka manyan gobe (7)

Tare da fatan alheri kuma da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin Ado da Bala labarin yana nuna mugunta ba tad a kyau. A sha karatu lafiya.

Taku: Amina Abdullahi

Labarin Ado da Bala

Ado mutum ne mai tausayi da tsoron Allah. Yana da yaya Bala shi kuma mai son cin zali ne da ha’inci.
Rannan Ado ya je rafi sai ya ci karo da wani yaro yana kuka wai ya rasa hanyar gida. Sai Ado ya ba shi abinci ya ce da shi zai kai shi gida. Sai yaron ya bace ya zama fatalwa. Ya ce zai taimaka masa kamar yadda ya taimaka shi.
Ya ba shi kudi da dama da wani sanda.
A kan hanyar Ado ta komawa gida sai ya ci karo da barayi suka kwace masa kudin. Yana hura sandan sai barayi suka yi bacci ya je ya kwashe dukiyarsa.
Ya dawo gida ya bai wa Bala labari.
Shi ma ya je rafi sai ya ga wata tsohuwa. Ya ce tab! Shi yaro kawai zai taimaka wa.
Haka ya koma gida talauci ya addabe shi.
Yaje gidan Ado ya sace sanda ya je gidan sarki ya yi sata. Ya zata sandar za ta yi aiki ne, amma dogarai suka kama shi saka rufe shi a kurkuku.