barnar kindirmo

Wani Bafulatani ne ya ziyarci birni kuma da isarsa sai ya tarar da wani gida yana sheki, an yi masa farin fenti gwanin ban sha’awa.  Ya samu waje ya zauna, ya zuba wa gidan ido sai sharbar kuka yake. Mutane suka taru a kansa don jin dalilin da ya sa yake kuka. Da kyar aka […]

barnar kindirmo
barnar kindirmo

Wani Bafulatani ne ya ziyarci birni kuma da isarsa sai ya tarar da wani gida yana sheki, an yi masa farin fenti gwanin ban sha’awa.  Ya samu waje ya zauna, ya zuba wa gidan ido sai sharbar kuka yake. Mutane suka taru a kansa don jin dalilin da ya sa yake kuka. Da kyar aka shawo kansa ya fadi dalili kamar haka: “Wallahi wulakancin mutanen birni ne ya sa ni kuka, yanzu a ce a rasa inda za a yi barnar kindirmo sai a wannan gida. Dubi yadda aka bi shi da kindirmo aka shafe sai kyalli yake kamar ba su san darajar kindirmo ba!”
Daga Ahmed Garba Mohammed, 08028797883

An gano baƙin haure 30 a ɓoye cikin tankar mai a Turkiyya

An tsare ɗan gwagwarmaya kan sukar gwamnatin sojin Nijar

Alhazan Kebbi rukunin farko sun dawo gida

Rukunin farko na Alhazan Kebbi 426 sun dawo gida