Basarake ya bukaci Buhari ya basu makamai a yaki barayin Zamfara
Mai Martaba Sarkin Anka kuma shugaban majalisar Sarakunan jihar Zamfara Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta samar masu da makamai wadanda suka hada da bindogogi kirar AK 47 don magance kisan gilla da yin garkuwa da ake yi da jama’a a jihar. Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da yake kaddamar […]
Mai Martaba Sarkin Anka kuma shugaban majalisar Sarakunan jihar Zamfara Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta samar masu da makamai wadanda suka hada da bindogogi kirar AK 47 don magance kisan gilla da yin garkuwa da ake yi da jama’a a jihar.
Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da yake kaddamar da rabon Babura 850 ga sababbin jami’an tsaron farin kaya da aka horar ‘Civilian Joint Task Force’ a jihar.