Basarake ya kare sojoji kan sukan da Amnesty ke yi musu
Daya daga cikin sarakunan Yarbawa Olowu na Owu-Kuta a Jihar Osun, Mai martaba Oba Hameed Adekunle Makama Oyelude, ya gargadi Kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Duniya ta daina sukar sojojin Najeriya a kan matakan da suke dauka na murkushe ayyukan ta’addanci na Boko Haram. Sarkin ya ce, “Na ga tura ta kai bango a […]
Daya daga cikin sarakunan Yarbawa Olowu na Owu-Kuta a Jihar Osun, Mai martaba Oba Hameed Adekunle Makama Oyelude, ya gargadi Kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Duniya ta daina sukar sojojin Najeriya a kan matakan da suke dauka na murkushe ayyukan ta’addanci na Boko Haram.
Sarkin ya ce, “Na ga tura ta kai bango a kan yawan sukan da masu kare hakkin dan Adam suke yi ga sojojinmu shi ne ya sa na kira taron ’yan jarida na duniya domin mu nuna musu cewa muna tare da sojojin kuma ba za mu amince da kungiyoyin su karya musu gwiwa ba.”
Oba Adekunle Makama ya fadi haka ne a ranar Alhamis ta makon jiya a wajen taron manema labarai na duniya a fadarsa da ke garin Kuta, inda ya nuna bacin ransa a kan yadda kungiyoyin kare hakkin dan Adam na duniya suke yi wa sojojin Najeriya taron dangi.
Ya ce, “Wadannan sojoji ’ya’yanmu ne da suke sadaukar da rayukansu cikin dare da rana suke shiga cikin dazuka domin tsare kasarmu Najeriya. Ba za mu taba amincewa da wannan suka da Kungiyar Amnesty International take yi ga sojojinmu ba. Ina shaida wa wadannan kungiyoyi cewa abin da suke yi, ya isa kuma ya isa!”
Sarkin wanda shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Masarautar Owu-Kuta, ya yi tambayar cewa, “Me ya sa wadannan kungiyoyi ba sa yin magana a kan wasu kasashen duniya da al’amarin ta’addanci ya kazanta? Wato Najeriya kadai suka raina suke yi mata taron dangi domin ’yan ta’addan Boko Haram su ci karensu ba babbaka.”
Aminiya ta tambayi Sarkin cewa ko mene ne dalilin mayar da martanin da yake yi kuma wane mataki za su dauka? Sai Oba Adekunle Makama ya ce “Kwanan baya Kotun Duniya (ICC) da ke Hegue na kasar Holand ta fito da rahoton wannan shekara, inda ta nuna cewa sojojin Najeriya suna take hakkin dan Adam a kan ’yan Boko Haram. Duk bayanan rahoton da mai gabatar da kara ya gabatar wa Kotun ICC a kan wannan al’amari an tattara shi ne daga bayanan da Kungiyar Amnesty ta mika musu wanda ba mu yarda da shi ba.”
“Dangane da matakin da za mu dauka kuwa, ina kira ga sarakuna ’yan uwana da attajirai da masana harkokin diflomasiya da ’yan siyasa da dukan al’ummar Najeriya mu jingine siyasa waje daya mu fito kwai da kwarkwata mu kalubalanci wannan mataki da kungiyoyin suke dauka na bata sunan Najeriya. Ina yi musu kashedin cewa idan har suka ki sauya salon wannan tafiya, to za mu umarci dukan al’ummar Najeriya su kyamace su, kuma su mayar da martani. Yanzu haka Fadar Olowu na Owo-Kuta ta fara daukar wannan mataki na yaki da kungiyoyin kare hakkin dan Adam na duniya,” inji shi.
Ya bukaci kafafen watsa labari su guji yada rahotannin kungiyar da ka iya jefa kasar nan a cikin hadari. “Idan kun ga wani abu da zai nakasa sojojinmu ku daina rubutawa a jaridunku.” inji Olowu na Owu-Kuta.