Basarake ya kyautar wa talakawansa 600 da amfanin gonarsa

Ya bukaci talakawan nasa da su yi amfani da buhunan hatsin da ya ba su wajen ciyar da iyalansu

Basarake ya kyautar wa talakawansa 600 da amfanin gonarsa

Manoma

Basaraken yankin Bakundi da ke Ƙaramar Hukumar Bali a Jihar Taraba, Alhaji Inuwa Muhammad Musa, ya ba wa talakawansa kimanin mutum 600 kyautar duk amfanin da aka girbe a wata gonarsa mai faɗin hekta 10.

Alhaji Inuwa Mohammed Musa ya gwangwaje talakawan nasa ne da buhu biyu na hatsi kowannensu a matsayin tallafin rage musu raɗaɗin tsadar rayuwa da yunwa.

Da farko Alhaji Inuwa ya gayyaci talakawan nasa ne zuwa aikin gayya domin girbe gonar masarar, inda wasu daga ƙalilan da cikinsu su ka amsa goron gayyatar.

Bayan abin da kowanne daga cikinsu ya haɗa ya kai buhu biyu, sai ya shaida musu cewa da ma ya gayyato su ne domin ya yi musu kyautar hatsin domin rage musu raɗaɗin tsadar rayuwa da yunwa da ake ciki.

Daga nan ya yi musu izinin tafiya gida da ita, tare da ba su shawarar kada su sayar.

Ya ce , “Ina ba ku shawara ku yi amfani da ita wajen ciyar da iyalanku da buhu biyu-biyu na masara da kowannenku ya samu.

“Manufar ba ku ita ce domin ku samu abin da za ku ciyar da iyalanku, saboda na san kuna cikin fama da matsin rayuwa.”

Labarin na kaiwa cikin garin na Bali, sai daruruwan mutane suka yi ta tururuwar zuwa gonar da ke yankin Galadima Ajuji.

An ƙiyasta cewa yawan waɗanda suka amfana da kyautar ya kai mutum 600.

Alhaji Inuwa Muhammad Musa ya bayyana cewa ya sadaukar da amfanin gonar ne a matsayin tallafi ga talakawansa da kuma nuna godiyarsa ga Allah da Ya kare gonakinsa guda takwas daga fari da ta shafi yawancin gonakin yankin.

Ya ce manufarsa ita ce sama wa al’umma saukin abin da za su ci a wannnan yanayin na yunwa da tsadar kayan abinci.

Wasu daga cikin mutanen yankin da suka amfana da wakilinmu ya zanta da su sun bayyana godiyarsu ga Allah bisa wannan karimci na basaraken.

Sun kuma yi kira da sauran mawadata da su yi koyi da shi.

Wani dattijo mai shekaru 58, Bana Hurumin, ya ce a tsawon rayuwarsa bai taba sanin wani basarake da ya yi irin wannan abin alheri ba a fadin yankin Bali.

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu