Basarake ya rantse da Alkur’ani a masallaci cewa ba ya taimaka wa ’yan bindiga
“Matukar ina taimaka musu, kada Allah ya sa na kai wani satin,” inji shi.
A Jihar Sakkwato, wani basarake ya mike a masallacin Juma’a sannan ya rantse da Alkur’ani mai girma kan cewa ba ya taimaka wa ayyukan ’yan bindiga ta kowacce fuska a masarautarsa.
Basaraken, wanda shi ne Hakimin Isa, kuma Sarkin Gobir din Isa, Alhaji Nasir Ahmad ya rantse da Alkur’anin ne a masallaci biyo bayan zargin da wasu mazauna yankin ke yi masa na alaka da ’yan ta’adda.
- Rashin man fetur ya sa ’yan bindiga sun koma amfani da rakuma a Sakkwato
- ’Yan bindiga sun kashe mutane da dama a sansanin sojoji a Sakkwato
Ko a ranar Litinin din da ta gabata sai dai wasu fusatattun mazauna yankin suka kai hari kan fadar Hakimin bayan sun zarge shi da ba bata-gari mafaka.
Rahotnanni sun ce Hakimin ya mike a Masallacin Juma’ar garin jim kadan kafin fara Salla sannan ya rantse cewa ba ya taimaka wa ayyukan ta’addanci.
“Idan na taba taimaka wa kowanne irin hari a yankina, ko na taba ba ’yan bindiga bayanai a kan ayyukan sojoji a masarautata, kada Allah ya sa na kai wani makon,” inji shi.
A wani faifan bidiyon Hakimin dai wanda ya karade gari musamman a kafafen sada zumunta na zamani, an jiyo Hakimin na cewa ya fi kowa a yankin jin takaicin hare-haren da ake kai wa jama’arsa.