Basarake ya soki dan acaba da wuka ya kwace babur dinsa

Hakimin garin Balu karama da ke karamar Hukumar Bunza a Jihar Kebbi Malam Garba Bagudu (Guru), ya fada hannun jami’an tsaro bisa zarginsa da daba wa wani dan acaba wuka inda ya kwace babur dinsa.Wani da bai so a bayyana sunansa ya shaida wa wakilinmu a garin Bunza cewa hakimin ya dauki shatar dan acabar […]

Basarake ya soki dan acaba da wuka ya kwace babur dinsa
Basarake ya soki dan acaba da wuka ya kwace babur dinsa

Hakimin garin Balu karama da ke karamar Hukumar Bunza a Jihar Kebbi Malam Garba Bagudu (Guru), ya fada hannun jami’an tsaro bisa zarginsa da daba wa wani dan acaba wuka inda ya kwace babur dinsa.
Wani da bai so a bayyana sunansa ya shaida wa wakilinmu a garin Bunza cewa hakimin ya dauki shatar dan acabar ne daga kauyen Gumki a karamar Hukumar Arewa inda yake zuwa caca don kawo shi kauyensa, amma suna wuce kauyen Rafin -Tsaka sai hakimin ya soka wa dan acabar wuka a ciki bayan sun fadi sai hakimin ya dauke babur din ya koma ta inda suka fito.  
Ya ce Allah Ya kaddara dan acabar bai mutu ba, sai ya buga wa ’yan uwansa waya ya gaya musu abin da ya faru kuma ya gaya musu cewa ta hanyar ya koma, daga nan sai ’yan uwan suka zo kan hanya suka tsaya yana zuwa suka kama shi.
 Lokacin da wakilinmu ya tuntubi babban jami’in ’yan sandan yankin ta waya bai dauka ba, amma jami’in watsa labarai na karamar hukumar Buhari Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce tuni aka cire shi daga sarauta, kuma an tura keyarsa gidan yari kafin yi masa shari’a.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi