Bashar Lawal Zakka, Birnin Kebb

’Yan bindiga dauke da bindigogi da kuma bam sun kashe dalibai masu yawa a Kano, a wani hari da suka kai Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya da ke Kano. Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar mutum 15 da suka hada da ’yan kunar bakin wake biyu da suka rasu a yayin da […]

Bashar Lawal Zakka, Birnin Kebb
Bashar Lawal Zakka, Birnin Kebb

’Yan bindiga dauke da bindigogi da kuma bam sun kashe dalibai masu yawa a Kano, a wani hari da suka kai Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya da ke Kano. Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar mutum 15 da suka hada da ’yan kunar bakin wake biyu da suka rasu a yayin da suka bude wuta a kan daliban da suke cikin manyan dakuna daukar lacca biyu na kwalejin.  ’Yan sandan sun ce maharan biyu sun kashe kansu da bam kuma an gano bindigoginsu biyu kirar AK-47, a wurin harin. Sai dai kuma mutanen da ke kusa da kwalejin sun cewa yawan mutanen da suka rasu sun fi haka yawa, a cikinsu har da jariran da ake ganin na wasu dalibai mata ne da abin ya rutsa da su. Wani da bai so a bayyana sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa “Ni dalibin makarantar ce kuma muna dab da shiga ni da abokin karatuna abin ya faru, inda muka rika jin harbe-harbe daga cikin makarantar.” Ya ce jin haka sai suka koma da baya. Wasu da suka ce sun ga mutane suna gudu a lokacin faruwar lamarin, sun ce ana zargin wadanda suka kai harin sun je ne a cikin kakin soja. Kuma sun ce sai bayan kimanin awa daya da kai harin ne jami’an tsaro suka isa wurin, ba tare da sun kama kowa ba.  Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano, Aderenle Shinaba ya bayyana wa manema labarai cewa mutum 15 suka rasu, kuma 43 sun samu raunuka. Harin dai ya faru ne da misalin karfe 2:00 na rana a shekaranjiya Laraba lokacin da ake kai-komo kuma kwalejin ke cike da dalibai da malamai da ma’aikata, kuma harin ya kidima mutane da dama tare da jefa fargaba a zukatan jama’a, musamman iyayen dalibai da ke karatu a kwalejin. Bayanai sun ce dalibai da dama sun ji rauni ko rasu ne a yayin da suke kokarin tsira daga habe-harben da karar bama-baman ’yan kunar bakin wake da maharan biyu suka tayar bayan bude wa daliban wuta. Makwabtan kwalejin da na unguwannin Kabuga da Sani Mainagge da ’yan kasuwar da ke kusa da kwalejin da masu wucewa da ababen hawa da kafa sun firgita suka rika gudun neman mafaka.
Wannan shi ne karo na uku da ake kai hari a kan manyan makarantu a cikin birnin Kano a bana. Kimanin wata biyu da suka gabata wata mace ’yar kunar bakin wake ta tayar da bam ta kashe kanta da wasu dalibai a kofar Makarantar Kimiyya da kere-kere ta jihar. Watanni hudu baya an kai wa daliban makarantar koyon aikin tsabta ta jihar hari, lokacin da suke je karbar sakamakon jarrabawarsu.