Bashin biliyan 7 naci don biyan albashin watan Mayu- Gwamnan Ogun
Gwamnan jihar Ogun Prince Dapo Abiodun ya bayyana cewa, kalubalen da ya soma fuskanta a lokacin da aka rantsar da shi a matsayin Gwamna shi ne yadda zai biya albashin ma’aikatan jihar, kasancewar bai tarar da komai ba a lalitar gwamnatin jihar. Gwamnan ya shaida haka ne a zama na musamman da ya yi da […]
Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun
Gwamnan jihar Ogun Prince Dapo Abiodun ya bayyana cewa, kalubalen da ya soma fuskanta a lokacin da aka rantsar da shi a matsayin Gwamna shi ne yadda zai biya albashin ma’aikatan jihar, kasancewar bai tarar da komai ba a lalitar gwamnatin jihar.
Gwamnan ya shaida haka ne a zama na musamman da ya yi da shugabanin jam’iyar APC na jihar a jiya Litinin inda ya fayyace masu kamun ludayin gwamnatin sa cikin wata guda tare da bayyana masu inda yake so ya dosa.
Gwamna Abiyodun, ya ce tun da fari ya riga ya yi alkawarin bazai bibiyi lamurran gwamnatin da ta gabata ba, don haka ya shata layi babu ruwan sa dai waiwayar baya, “Domin bamu da lokacin batawa zamu mai da hankali ne ga ayyukan da zamu yi wa jama’a, babu batun tune-tunen abubuwan da suka shude, babban kalubalen da na fara fuskan ta a matsayin na na gwamna shi ne yadda zan biya albashin watan Mayu, kamar yadda na yi alkawarin biya akan kari, mun kama aiki a ranar 30 ga watan, mun shiga gwamnati ba mu iske komi ba ganin haka sai na kira wasu abokai na manyan manajojin banki su biyar na nemi su hada min bashin sama da Naira biliyan 7 domin na biya albashin ma’aikata a haka suka hada min kudin, kuma cikin yardar Allah ma’aikatan mu suka sami albashin su a yammacin ranar 31 ga watan Mayu kamar yadda muka yi masu alkawari”. In ji shi.
Ya ce, akwai aiki tukuru a gaban sa don haka ya shata layi ga abubuwan da suka wuce domin ya samu cikakken lokacin yi wa al’ummar jihar aiki.