Bashin da aka ba kamfanonin wutar lantarki ba zai sa a kara kudin wuta ba- Ministan wutar lantarki

Ministan wutar lantarki Farfesa Chinedu Nebo ya ce bashin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ba kamfanonin samar da wutar lantarki da kuma rarrabata ba zai sanya a kara kudin wuta ba. Idan ba a manta ba Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ba kamfanonin rarraba wutar lantarki 5 (Discos) da kuma kamfanonin samar da wutar […]

Bashin da aka ba kamfanonin wutar lantarki ba zai sa a kara kudin wuta ba- Ministan wutar lantarki
Bashin da aka ba kamfanonin wutar lantarki ba zai sa a kara kudin wuta ba- Ministan wutar lantarki

Ministan wutar lantarki Farfesa Chinedu Nebo ya ce bashin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ba kamfanonin samar da wutar lantarki da kuma rarrabata ba zai sanya a kara kudin wuta ba.

Idan ba a manta ba Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ba kamfanonin rarraba wutar lantarki 5 (Discos) da kuma kamfanonin samar da wutar lantarki 3 (Gencos) bashin Naira biliyan 18 don ganin wadannan kamfanoni sun tsaya da kafafunsu a bangaren kasuwanci.
A lokacin da yake jawabi a wurin taron a Abuja a ranar Litinin Gwamnan Babban Bankin Najeriya Mista Godwin Emefiele ya ce bankinsu ya yanke hukuncin ba da wannan bashin ne sakamakon karancin kudin shiga da ke addabar bangaren kamfanonin da suke da ruwa da tsaki a wutar lantarki a kasar nan.
Ya bayyana kamfanonin za su biya bashin da aka ba su nan da shekara 10 a kan kudin ruwa mai kashi 10 cikin 100.
Ya ce kamfanonin Discos da suka fara amfana da wannan bashin sun hada da na Eko (bashin Naira biliyan 5.16) da na Ibadan Discos (bashin Naira biliyan 11.37.
Kamfanonin Gencos sun hada da Jaba wanda aka ba bashin Naira miliyan 816 da ba Jebba wanda ya karbi bashin miliyan 234 sai na Kainji wanda ya karbi bashin miliyan 678.
Gwamnan ya bayyana wadannan kamfanoni da aka fara ba bashin su ne suka fara cika dukkan ka’idar da ake bukata.
“Ina fata sauran kamfanonin za su yi koyi da wadannan kamfanoni da muka fara ba bashi ta hanyar cika dukkan ka’idojin da ake bukata kafin su karbi basussukan da suke bukata.”
Ministan Wutar Lantarki Farfesa Chinedu Nebe ya ce kamfanonin sun shiga wannan matsaloli ne sakamakon kuskuren lissafin yadda za su tafiyar da kamfanoninsu tun bayan da harkar wutar lantarki ta koma hannunsu.
Ya tabbatar wannan bashin ba zai sa a kara kudin wuta ba, amma zai taimaka wa kamfanonin su kara inganta harkokinsu.
“Wannan matsalar ta faru ne sakamakon kuskuren lissafi da kamfanonin da harkar wutar lantarki ta koma wurin suka yi, musamman ma ta bangaren yadda za su tafiyar da harkokinsu. Amma wannan bashin zai sanya su tsaya da kafafunsu. Bashin ba zai sa a kara kudin wuta ba.” Inji shi.