Bashin da ake bin Najeriya ya karu zuwa tiriliyan 40

Adadin ya hada da na Gwamnatin Tarayya da na jihohi da ma Babban Birnin Tarayya Abuja

Bashin da ake bin Najeriya ya karu zuwa tiriliyan 40

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Ofishin kula da Basussuka na Kasa (DMO) ya ce yawan basshin da ake bin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 39.56, wato Dala biliyan 95.78 a karshen watan Disamban shekarar 2021.

Darakta-Janar ta Ofishin, Mis Patience Oniha, ta bayyana cewa adadin shi ne jumullar bashin kudaden da ake bin Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi 36 da kuma Abuja, a cikin gida da wajen Najeriya.

Ko a kasafin kudin shekarar 2022 dai sai da Gwamnatin Tarayya ta tsara ciyo sabon bashin Naira tiriliyan 5.5 daga ciki da wajen kasa don aiwatar da wasu manyan ayyuka.

Misis Patience ta ce, “Za a ciyo sabbin basussukan ne daga wasu bankuna da cibiyoyin kudade na kasashen Turai kamar su Eurobond da Sukuk da sauransu. Za a yi amfani da su ne wajen wasu manyan ayyuka da tallafa wa tattalin arziki.”

Da take tsokaci a kan fargabar da ake yi kan katutun da bashi ke ci gaba da yi wa Najeriya katutu, Darakta-Janar din ta ce jimlar bashin bai wuce kaso 40 cikin 100 na adadin kudaden da ake tasarrufi da su ba, wato kasa da abin da kasar ta shardanta wa kanta.

“Idan ma aka yi la’akari da sharadin Bankin Duniya da na Asusun ba da Lamuni na Duniya (IMF) na kaso 55 cikin 100 ga kasashe makamantan Najeriya, za a ga babu wani abin fargaba a ciki.

“Gwamnatin Tarayya na matukar taka-tsantsan da karuwar basussukan, kuma tana bullo da sabbin dabarun habaka hanyoyin samun kudaden shiga, ciki har da kirkiro sabuwar Dokar Kudade ta 2019,” inji ta.