Bashin da Bankin Duniya zai ba yankin Arewa-maso-Gabas

A wani mataki na agaza wa yankin Arewa-maso-Gabas wajen sake gina yankunan da ’yan kungiyar Boko Haram suka lalata a tsawon shekaru shida, a makon jiya ne Bankin Duniya ya bayyana shirinsa na taimaka wa yankin da Dala biliyan biyu da miliyan 100 domin sake gina tattalin arzikin yankin. Jami’an bankin sun ce kudin za […]

Bashin da Bankin Duniya zai ba yankin Arewa-maso-Gabas
Bashin da Bankin Duniya zai ba yankin Arewa-maso-Gabas

A wani mataki na agaza wa yankin Arewa-maso-Gabas wajen sake gina yankunan da ’yan kungiyar Boko Haram suka lalata a tsawon shekaru shida, a makon jiya ne Bankin Duniya ya bayyana shirinsa na taimaka wa yankin da Dala biliyan biyu da miliyan 100 domin sake gina tattalin arzikin yankin.

Jami’an bankin sun ce kudin za a yi amfani da su ne wajen sake gina yankin ta hanyar Hukumar Ci gaban kasashe wato (IDA) wadda take bai wa gwamnatoci bashi da karancin ruwa.
Kamar yadda suka bayyana, shekarun goman farko bayan karbar bashin, ba za a biya kudin ruwan ba. Kuma kudin ruwan da za a biya a shekaru 30 masu zuwa ba za su kai na bashin da aka saba ba da wa ba.
Jihohin Barno da Yobe da kuma Adamawa su ne wadanda rikicin ya fi shafa, wuraren da dubban mutane suka rasa rayukansu kuma fiye da mutum miliyan guda suka kaurace wa muhallinsu.
An bayyana aniyyar taikawa da kudin ne ta bakin babban jami’in bankin, a makon jiya, lokacin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara kasar Amurka, lokacin wani taro da Gidauniyar Bill and Melinda Gates. Taron wanda har ila yau, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta hallarta, a cewar daya daga cikin kakakin Shugaba Buhari, Mista Femi Adesina ya bayyana.
Ya ce shugaban ya yi bayanin cewa baya ga sake gina yankin ta fuskar abubuwan more rayuwa, za a bai wa kara tsugunar da ’yan gudun hijiran wadanda suke zaune a sansanonin ’yan gudun hijira fifiko.
Shugaba Buhari ya bukaci Bankin Duniyan da ya tura wata tawaga yankin wadda za ta gana da jami’an gwamnatin tarayya domin gano hakikanin bukatun yankin.
Tallafin Bankin Duniyar da kuma sauran hukumomi, abu ne da ya dace musamman a wannan lokaci da yankin Arewa-maso-Gabas yake matukar bukatar taimako. Kodayake, kudin bashi ne, ba kyauta ba. Taimakon kasashen duniya da na gwamnati suna da iyaka, matukar kungiyoyin ’yan kasuwa da kungiyoyi masu zaman kansu ba su bayar da nasu taimakon ba a yankin da rikici ya shafa.
Kamar yadda muka sha fadi a baya, yakamata ya yi a kirkiri wani shiri don taimaka wa yankin, kwatankwacin irin wanda kasar Amurka ta jagoranta bayan kawo karshen yakin Duniya na Biyu.
Asibitoci da makarantu da kuma gadoji misalai ne na wasu abubuwa da a yanzu ba a iya samu a wadannan yankunan. Wannan ya sa akwai bukatar sake da dawo da su, idan so samu ne ma a kara inganta su daga matsayinsu na baya.
Kudin tallafin ko da nawa ne ba zai magance dukkan matsalolin al’ummar yankin ba, wannan ya sa akwai bukatar karin taimako. Kamar yadda shugaban kasa ya bayyana, yakamata a bai wa kara tsugunar da ’yan gudun hijira muhimmanci don su samu damar ci gaba da rayuwa.
Idan kuma ana so a samu nasara, to yakamata a sanya ido kan yadda za a kashe kudin don tabbatar da kashe su ta hanyar da ta dace.
Ya dace a ce tun daga farkon shirin a tabbatar da cewa mutane masu rikon amana, wadanda suke kishin yankin, masu jajircewa don gudanar da aikin. Wannan ya dace ne don kauce wa saiko da kuma cikas.
A wannan lokacin, kowane dakika guda yana da muhimmacin musamman idan za a yi amfani da shi wajen aikin jin kai.
Yakamata tallafin Bankin Duniya ya zama somin tabin taimakon da za a kai wa yankin Arewa-maso-Gabas, wanda kuma hakan zai nuna wa ’yan gwagwarmayar cewa zaman lafiya ne kawai zai iya kawo ci gaba, amma ba kashe-kashe ko lalata dukiya da suke yi yau tsawon shekaru.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50