Bashin da Kwankwaso ya bari ba abin damuwa ba ne – Ganduje
Sabon Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya ce bashin Naira biliyan 300 da tsohon Gwamnan Jihar Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya bari ba wata matsala ba ce idan aka dubi irin ayyukan da gwamnatin ta gudanar a fadin jihar cikin shekara hudu da ta yi tana mulki. Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana […]
Sabon Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya ce bashin Naira biliyan 300 da tsohon Gwamnan Jihar Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya bari ba wata matsala ba ce idan aka dubi irin ayyukan da gwamnatin ta gudanar a fadin jihar cikin shekara hudu da ta yi tana mulki.
Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana haka ne a zantawarsa da manema labarai a Kano, inda ya ce duk ayyukan da aka gudanar tare da shi aka yi su, don haka batun cewa toshon Gwamna Kwankwaso ya bar masa bashi ba wani abu ba ne sabo.
Dokta Ganduje ya ce ayyukan da toshon Gwamna kwankwaso ya gudanar a jihar kano suna da tarin yawa da kuma muhimmanci ga al’umma ’ya’ya da jikoki, don haka a cewarsa bashin da aka bari ba wani abin korafi ba ne kuma da yardar Allah zai ci gaba da aiwatar da ayyuka masu amfani ga al’ummar jihar ba tare da tsaiko ba.
Gwamna Ganduje ya ce gwamnatinsa za ta dora daga inda ta Kwankwaso ta ajiye ta yadda za a cimma manufofin da suke kai na aiki domin al’ummar Jihar Kano, kuma ya yi fatan za a ba gwamnatin cikakken goyon baya da hadin kai domin kaiwa ga nasara.
A wani labarin kuma, Gwamna Ganduje ya ba ’yan kwangilar da ke gudanar da ayyuka a jihar umarnin su ci gaba da ayyukansu domin ganin an kammala daukacin ayyukan da gwamnatin da ya gada ta faro, kafin fara aiwatar da wasu manufofi na gwamnatinsa.
Ya nanata kudurin gwamnatinsa na kara karfafa shirin tsaftar muhalli domin tabbatar da tsabtace birnin Kano da kewaye yadda ake bukata, inda ya sanar da cewa gwamnatinsa za ta dawo da aikin duba-gari ta hanyar daukar maza da mata aikin kula da tsabtar muhalli domin cimma nasarar shirin.