Bashin hadakar tarho: NCC ta bayar da tabbacin kare masu amfani da tarho

Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta bayar da tabbacin kariya ga fiye da mutum miliyan 174 da ke amfani da tarho  daga duk wani tsaikon kira daga shiga tsakanin da hukumar ke yi a yanzu don warware karuwar bashin hadaka na kira a tsakanin kamfanonin tarho a kasa baki daya. Hukumar ta yi kira ga […]

Bashin hadakar tarho: NCC ta bayar da tabbacin kare masu amfani da tarho
Bashin hadakar tarho: NCC ta bayar da tabbacin kare masu amfani da tarho

Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta bayar da tabbacin kariya ga fiye da mutum miliyan 174 da ke amfani da tarho  daga duk wani tsaikon kira daga shiga tsakanin da hukumar ke yi a yanzu don warware karuwar bashin hadaka na kira a tsakanin kamfanonin tarho a kasa baki daya.

Hukumar ta yi kira ga kamfanonin da ake bi bashi su biya bashin da sauran kamfanoni ke binsu ba tare da bata wani lokaci ba  don kaucewa raguwar samun kudin shiga da kaurar masu amfani da tarho daga kamfanoninsu zuwa wadansu kamfanonin.

Mataimakin Shugaban Hukumar, Farfesa Umar Dambatta ne ya yi furucin a Abuja inda ya ce Hukumar NCC ta himmatu wajen ganin masu amfani da tarho sun ci moriyar kira ba tare da wani tsaiko ba.

Ya ce kokarin da hukumar na yin kokari ne don ganin ta warware batun bashi a masana’antar baki daya.

Farfesa Dambatta ya ce hadakar kira wani batu ne Hukumar ke kokarin warwarewa don kare abokan hulda ta hanyar tabbatar da ingancin kiran da suke yi bai samu tsaiko ba.

Mataimakin Shugaban ya ce yayin da Hukumar ke bayar da ummarnin yanke kiran wanda suke bi bashi a shekarar da ta gabata a matsayin wata dama ta karshe ta sasanta bashin hadakar wanda ke yin barazana ga lafiya da dorewar masana’antar.

“Kodayake hukumar ta amince da bukatar kamfanin sadarwa na MTN na yanke sadarwar duk wani kamfani da yake bi bashi bisa dokar sashi na 100 na dokar sadarwa ta Najeriya ta shekarar 2003, tsarin na amincewa da ummarnin yanke sadarwa duk wani kamfani a shekarar 2012 da sauran tsare-tsaren sanya ido, abin da ke faruwa yanzu shi ne kamfanonin da ke bin bashi na toshe sadarwar kamfanonin da suke bi bashi ta hanyar yanke sadarwasu kai tsaye,” inji shi