Bashin Naira biliyan bakwai na bari ba biliyan 46 ba – Shinkafi

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Mahmuda Aliyu Shinkafi, ya yi watsi da zargin da gwamnatin jihar ke yi cewa ya bar bashin Naira biliyan 46 a lokacin da ya mulkin jihar.Alhaji Mahmud Shinkafi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau bayan kammala taron dattawan Jam’iyyar PDP a karshen […]

Bashin Naira biliyan bakwai na bari ba biliyan 46 ba – Shinkafi
Bashin Naira biliyan bakwai na bari ba biliyan 46 ba – Shinkafi

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Mahmuda Aliyu Shinkafi, ya yi watsi da zargin da gwamnatin jihar ke yi cewa ya bar bashin Naira biliyan 46 a lokacin da ya mulkin jihar.
Alhaji Mahmud Shinkafi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau bayan kammala taron dattawan Jam’iyyar PDP a karshen mako.
Ya ce wannan zargi soki burutsu ne kawai domin a bata masa suna a idon al’ummar jihar, inda ya ce a saninsa ya bar bashin Naira biliyan biyar ne kacal, tare da ruwa na Naira biliyan biyu, jimilla ya zama Naira biliyan bakwai.
Ya ce gwamnatin Alhaji Abdul’aziz Yari ta tattara wasu daga cikin kwangilolin da bai kammala
ba da ayyukan kananan hukumomi da ba a kammalaba, ta tattara jimillar kudin ya ba ta Naira biliyan 46, take yayatawa a matsayin bashi.
Alhaji Shinkafi ya ce zai so a ce Gwamnatin Abdul’aziz Yari ta bi bankunan da ke jihar don ta gano hakikanin bashin da ya bari don tabbatar da adalci, ba a rika zargi ana yada abin da ba gaskiya ba.