Bashin Najeriya ya karu zuwa Naira tiriliyan 21-Hukumar DMO
Darakta Janar na Hukumar Killata Bashin Najeriya, Patience Oniha ta ce a karshen watan Disemban shekarar 2017 bashin kasar ya karu zuwa Naira tiriliyan 27 da digo 7 kwatankwacin Dala biliyan 70 da digo 92. Ta ce cikin watan Juli gwamnati za ta biya tsarin nan na Eurobond idan ya bunkasa. Dimbin bashin […]
Darakta Janar na Hukumar Killata Bashin Najeriya, Patience Oniha ta ce a karshen watan Disemban shekarar 2017 bashin kasar ya karu zuwa Naira tiriliyan 27 da digo 7 kwatankwacin Dala biliyan 70 da digo 92.
Ta ce cikin watan Juli gwamnati za ta biya tsarin nan na Eurobond idan ya bunkasa.
Dimbin bashin kasar na waje ya kai kashi 30 cikin dari sannan akwai kashi 70 na bashin gida bayan da aka tsayar da jarin Euroband na Dala biyu da digo biyar.
A farkon watan da muke ciki Najeriya ta biya basussukan da suka kai na Naira biliyan 130 a maimakon ta kyale basukan su ci gaba da gudana kamar yadda gwamnatocin baya suke yi.