Bashir Gatari ya bukaci hadin kan jama’ar mazabar Lere ta Yamma
Sabon dan Majalisar Dokoki ta Jihar Kaduna daga mazabar Lere ta Yamma Alhaji Bashir Gatari Idris ya bukaci al’ummar mazabar su tallafa masa wajen ba shi hadin kai da shawarwari domin ciyar da yankin gaba.Alhaji Bashir Gatari na Jam’iyyar APC ya bayyana haka ne a garin Lere, lokacin da yake zantawa da ’yan jarida jim […]
Sabon dan Majalisar Dokoki ta Jihar Kaduna daga mazabar Lere ta Yamma Alhaji Bashir Gatari Idris ya bukaci al’ummar mazabar su tallafa masa wajen ba shi hadin kai da shawarwari domin ciyar da yankin gaba.
Alhaji Bashir Gatari na Jam’iyyar APC ya bayyana haka ne a garin Lere, lokacin da yake zantawa da ’yan jarida jim kadan da bayyana sakamakon zaben da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata, inda ya ce babu abin da zai ce ga al’ummar mazabar Lere ta Yamma kan zabensa da suka yi, sai dai ya yi musu godiya da neman karin goyon bayansu.
“A lokacin yakin neman zabe na zagaya dukkan lungunan wannan mazaba kuma na ga irin matsalolin da suke damun al’ummarta, don haka zan yi iyakar kokarina wajen ganin an warware matsalolin, amma ina kira ga al’ummar mazabar nan su ci gaba da yi min addu’a tare da ba ni shawarwari. kofata a bude take don amsar duk shawarwarin da za a ba ni don ci gaban wannan yanki,” inji shi.
Babban Jami’in Hukumar Zabe ta kasa (INEC) a karamar hukumar Rabi’u Abdulsalam Magaji ne ya bayyana Bashir Gatari Idris na APC a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbin na ranar Asabar a mazabar Lere ta Yamma bayan ya kayar da ’yan takara uku.
Da yake bayyana sakamakon zaben a garin Lere, jami’in ya ce, ’yan takarar da suka fafata a zaben su ne Jamilu Yakubu Sulaiman na Jam’iyyar ACPN wanda ya samu kuri’a 61 da Bashir Gatari Idris na Jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’a dubu 17 da 672 da Ahmed Mu’azu Lere na Jam’iyyar PDM wanda ya samu kuri’a 328 da kuma Dokta Mato Dogara na Jam’iyyar PDP
wanda ya samu kuri’a dubu 10 da 779. “Wannan ya nuna cewa Bashir Gatari Idris na Jam’iyyar APC ne ya lashe zaben da yawan kuri’a dubu 17 da 672,” inji shi.
To, amma a zantawarsa da ’yan jarida wakilin Jam’iyyar PDP a wajen tattara sakamakon zaben, Alhaji Jumare Tanimu Magaji ya ce ba su gamsu da yadda aka gudanar da zaben ba. Don haka za su sake tafiya kotu don su kalubalanci sakamakon zaben.