Bashir na kungiyar Enyimba ya murmure don tunkarar Rahimo

Dan wasan gaba na kungiyar wasan kwallo kafa ta Enyimba International, Abdurrahman Bashir ya warke sarai daga ciwon kokon gwiwar da ya samu wanda ya hana shi buga wasan farko da kungiyarsa ta Enyimba ta je ta yi da kungiyar kwallon kafa ta Rahimo a ci gaba da wasannin Zakarun Afirka(CAF). A wata sanarwa da […]

Bashir na kungiyar Enyimba ya murmure don tunkarar Rahimo

Abdulrahman Bashir da shudiyar riga tafe da kwallo

Dan wasan gaba na kungiyar wasan kwallo kafa ta Enyimba International, Abdurrahman Bashir ya warke sarai daga ciwon kokon gwiwar da ya samu wanda ya hana shi buga wasan farko da kungiyarsa ta Enyimba ta je ta yi da kungiyar kwallon kafa ta Rahimo a ci gaba da wasannin Zakarun Afirka(CAF).

A wata sanarwa da mahukuntan Kungiyar Enyimba suka saka a shafin Intanet na Goal.com sun ce zakakurin dan wasan gaban ya gama murmurewa sarai kuma ana sa ran zai buga wasan gaba da kungiyar za ta yi a karshen makon nan a garin Aba tsakaninta da kungiyar kwallon kafa ta Rahimo.

Bashir ya samu rauni ne a kokon gwiwarsa wanda ya tilasta masa zaman jinya, amma a halin yanzu ya dawo fagen wasa ’yan kwanaki kafin Enyimba ta karbi bakuncin kungiyar Rahimo daga kasar Burkina Faso.

Raunin ya sanya an cire  Bashir daga ’yan wasa 20 da suka halarci wasan da ya wakana a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso, tsakani Enyimba da Rahimo wanda kungiyar Enyimba ta sha kashi da ci daya da nema.

“Bashir ya warke sarai kuma a shirye yake don taka leda a wasan da za mu yi da Rahimo. Zuwa yanzu ya ci kwallaye da dama a wasannin da muka buga na sada zamunci, wannan wata babbar alama ce ta nasara a gare mu,” inji mai Magana da yawun kungiyar ta Enyimba wacce ake yi wa lakabi da People’s  Elephant.