Bassa/Jos ta Arewa: An fara jefa kuri’a a zaben cike gurbi
Mutane sun fara jefa kuri’a tun da misalin karfe 8 na safe a zaben cike gurbin dan Majalisar Wakilai mai wakilitar kananan hukumomin Bassa da Jos ta Arewa na Jihar Filato. Zaben na gudana ne a ranar Asabar bayan rasuwar dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin biyu. Abin da fim din Sanda zango na biyu […]
Mutane sun fara jefa kuri’a tun da misalin karfe 8 na safe a zaben cike gurbin dan Majalisar Wakilai mai wakilitar kananan hukumomin Bassa da Jos ta Arewa na Jihar Filato.
Wakilinmu ya zaga wasu rumfunan zabe da ke gundumar Naraguta Ward “B” inda ya iske jami’an zabe sun isa wurin da kayan zabe a kan lokaci.
A zagayen da wakilinmu namu ya yi a safiyar Asabar, ya samu an tsaurara matakan tsaro a daukacin rumfunan zabe da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa.