Bata-gari sun kashe jami’in kwastam a Jigawa

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta ce miyagu sun harbe jami’in Kwastam tare da raunata wani a Karamar Hukumar Ringim ta jihar a yayin da suke sintiri. Kakakin Rundunar, SP Abdu Jinjiri, ya tabbatarwa da manema labarai faruwar lamarin a ranar Litinin. Buhari ya ba da lamunin kashe $3.1bn domin bunkasa hukumar kwastam Kwastam sun […]

Bata-gari sun kashe jami’in kwastam a Jigawa

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta ce miyagu sun harbe jami’in Kwastam tare da raunata wani a Karamar Hukumar Ringim ta jihar a yayin da suke sintiri.

Kakakin Rundunar, SP Abdu Jinjiri, ya tabbatarwa da manema labarai faruwar lamarin a ranar Litinin.

“A ranar 25 ga watan Oktoba 2020 mun samu rahoton wasu bata-gari sun harbe wani jami’in Kwastam tare da raunata abokin aikinsa, yayin da suke sintiri a kauyen Kyarama.

“Sannan ana zargin cewa bata-garin sun yi awon gaba da makaman jami’an kwastam din”, inji Jinjiri.

Ya sanar da cewa rundunar ’yan sanda a jihar na ci gaba da fadada bincike domin gano wadasnda suka aikata laifin.

Fiye da ƙungiyoyi 60 sun yi zanga-zanga kan taron G7 a Faransa

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina