Bata-gari sun kone gidan rediyon Jihar Kogi
Wasu bata-gari sun kai hari a gidan rediyon Gwamnatin Jihar Kogi, inda suka kone shi, suka kuma yi awon gaba da kayayyakinsa.
Bata-gari sun kai hari a gidan Rediyon Jihar Kogi, inda suka kone shi, suka kuma yi awon gaba da kayayyakinsa.
Bata-gari sun far wa tashar Kogi Radio 90.5 FM da ke Ochaja a Karamar Hukumar Dekina harin ne a safiyar Talata, inda bata-garin suka lakada wa masu gadin tashar dukan kawo wuka, sannan suka rika cin karensu babu babbaka, sun kona muhimman kayayyaki.
“Bata-gari sun sace duk muhimman kayyayakin da ke tashar, har da wani janareto kirar Mikano wanda wani dan takarar gwamna a zaben da za a yi a watan Nuwamba bayar gudummawa, bayan da suka yi wa masu gadi duka kawo wuka”, in ji wani shaida.
Gwamnatin Jihar Kogi ta yi tir da harin, a wata sanarwa da kakakin ma’aikatar yada labaran jihar, Salawu Patience, ta fitar, amma ta ba da tabbacin cewa jami’an tsaro na aiki don kamawa da kuma gurfanar da bata-garin domin hana maimatuwar hakan.
- Dan shekara 38 ya zama shugaban majalisar Osun
- Kotu ta yanke wa fitaccen fasto hukuncin rataya a Ribas
Ta ce kwamishinan ma’aikatar, Kingsley Fanwo, tare da Darakta-Janar na hukumar yada labaran jihar, Alhaji Ojo Oyila Ozovehe sun ziyarci tashar a ranar alatar domin ganin irin barnar da aka yi.
Ta bayyana cewa dole aka rufe tashar domin babu yadda za ta ia gabatar da shirye-shirye a haka, sakamakon irin barnar da aka yi a harin, amma gwamnatin jihar na kokarin ganin an farfado da tasar nan ba da jimawa ba.
Wakilinmu ya so samun karin bayani daga kakakin ’yan sandan jihar Kogi, SP William Aya, amma jami’in bai amsa kiran wayan ko rubutaccen sakon da aka tura masa ba.