Bata-gari sun mayar da kasuwa wajen cinikin miyagun kwayoyi
Ana zargin wasu ‘yan kasuwan sSabon garin Zariya da neman maida kasuwar ta zama sansanin sayar da miyagun kwayoyi. Matsalar ta’annadi da miyagun kwayoyi da kayan maye a tsakanin matasa da matan aure na kara yawaita a yankin Zariya da kewaye. Hakan na faruwa ne a bisa zargin da ake yi na yadda kusan mafiya […]
Ana zargin wasu ‘yan kasuwan sSabon garin Zariya da neman maida kasuwar ta zama sansanin sayar da miyagun kwayoyi.
Matsalar ta’annadi da miyagun kwayoyi da kayan maye a tsakanin matasa da matan aure na kara yawaita a yankin Zariya da kewaye.
Hakan na faruwa ne a bisa zargin da ake yi na yadda kusan mafiya yawan masu gudanar da sayar da haramtattun magunguna da kwayoyi da Gwamnatin Jihar Kano ta koro ne suka dawo da matsuguninsu a kasuwar sabon garin Zariyan, wanda hakan ya sanya damuwa a zukatan al’ummar yankin.
Majiyarmu da ta tabbatar wa Aminiya, kuma wadanda ba su so a ambaci sunayensu ba, kuma suna daga cikin ‘yan kasuwan wasunsu ma ‘yan kwamitin zartarwa ne na masu sayar da magunguna a kasuwar, wanda wakilin namu ya tattauna da su cewa akwai korafe-korafe da dama akan haka, sai dai suna so jama’a su sani cewa korarrun masu sana’ar sayar da magunguna na Kano da gwamnatin jihar ta kora sune suka dawo kasuwar Sabon garin na Zariya, kamar Mista Jude da Lambat da kuma Donotus da Bitrus, kuma wadanda ake zargin suna da hanyoyin da suke bi don shigowa da wadannan haramtattun miyagun magunguna ba tare da an kama su ba, domin sukan sanya kwayoyin a kwalayen da ba za’a taba zaton suna ciki ba, kuma wani lokaci ba sa zuwa kasuwar sauke kayan sai da daddare, kuma da damar mu musan da haka sai dai mun yi kokarin jawo, ko shawartar shugabanmu, amma ya ki fahimta.
Don haka ka ga jama’a suka hadamu gaba daya suna yi mana kakkabar dan giginya an hada mu gaba daya cewar duk haka muke.
Kamar yadda a duk lokacin da Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris in yana jawabi yake kokawa da yawan ta’annati da miyagun kwayoyi da kayan sanya maye a tsakanin matasa da matan aure, tare da yin kira ga hukumomin da su kara kaimi, domin dakile ire-iren masu tafiyar da wannan mummunar sana’ar don ceto al’umma daga halaka.
Da Aminiya ta tuntubi Shugaban masu sayar da magani na kasuwar Sabon gari Zariya, Alhaji Rabiu Kaya ta wayar hannu ko yana da masaniyar irin abin da ke faruwa a kungiyarsu, sai ya amsa da cewa shi a saninsa da ana shigowa da irin wadannan miyagun kwayoyin, amma yanzu ba a shigowa da su, kuma idan muna wata tantama to mu zo mu yi bincike, domin ya gaji da bita-da-kullin da ‘yan jarida ke yi musu saboda haka ba shi da abin da zai kara cewa sai dai suna shirin daukar duk wani mataki da ya dace a kan ‘yan jarida ta kowane irin hanya, domin sun matsa musu tare da sa musu idanu akan sana’arsu.