batan dana ya sa na yarda ana satar mutane – Hajiya Karima
Wata mace mai suna Hajiya Karima Abubakar da ke Unguwar Wudilawa a birnin Kano da danta mai shekara 17 mai suna Musa Kabir ya bace kuma ta yi ta nema tare da cigiyarsa ta kafafe daban-daban ba ta same shi ba, ta ce ta hakkake cewa ana satar mutane a kasar nan.Matar wacce ta ce […]

Wata mace mai suna Hajiya Karima Abubakar da ke Unguwar Wudilawa a birnin Kano da danta mai shekara 17 mai suna Musa Kabir ya bace kuma ta yi ta nema tare da cigiyarsa ta kafafe daban-daban ba ta same shi ba, ta ce ta hakkake cewa ana satar mutane a kasar nan.
Matar wacce ta ce rabonta da ganin dan nata zai yi kimanin mako hudu, ta ce yaron na zaune ne da mahaifinsa da suka rabu. Ta ce yana aji na biyu ne a babbar sakandare ta Usman Bin Affan da ke Unguwar dorayi. Hajiya Karima ta ce ana kyautata zaton ya bace ne a ranar Juma’a 29 ga Nuwamba kuma tun daga wannan lokacin har yanzu ba a same shi ba. “A da ina jin labarin batan mutane amma ban san zafin haka ba, sai da dana Musa Kabir ya bata. Mun bincika duk gidajen ’yan uwanmu, sannan mun bincika a caji ofis-ofis na ’yan sanda da dama da wurin ajiye gawa na asibitoci da gidajen fursuna, tare da kai cigiyarsa a gidajen rediyo, amma har yanzu ba a samu labarinsa ba,” inji ta.
Ta ce mahaifin yaron Alhaji Kabir, mai sayar da motoci a kan titin IBB a Kano shi ma ya fada mata cewa ya yi iyakar kokarinsa wajen nemansa, kuma a yanzu ya sa ana ta yin addu’a don Ubangiji Ya bayyana shi. Ta kara da kira ga hukuma da ta magance al’amarin, ta hanyar gano masu yi tare da hukunta su, sannan mutane su taya ta da addu’a.