Batanci ga Annabi: Deborah ta wuce gona da iri —Farfesa Maqari
Maqari ya ce dole ne mutane su kiyayi ketara iyakar musulunci.
Limamin Babban Masallacin Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari, ya ce dalibar nan da yi batanci ga Manzon Allah (SAW) wato Deborah Samuel, ta wuce gona da iri.
Farfesa Maqari ya ce bai kamata a fara ganin laifin wadanda suka kashe ta ba, ba tare da an yi la’akari da girman katobarar da ta aikata.
- Yawan Amurkawan da ke neman ‘tallafin zaman kashe wando’ ya karu sosai
- FIFA ta amince a sake doka wasan Argentina da Brazil da ta dakatar a bara
Deborah ’yar aji biyu a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Wamako a Jihar Sakkwato, ta gamu da ajalinta ne a hannun abokan karatunta, bayan da ta furta kalaman batanci ga Manzon Allah (SAW).
Maqari, ta shafinsa na sada zumunta, ya ce an kashe matashiyar ne saboda ta ketara iyakar Musulunci wajen yin bataci ga Fiyayyen Halitta.
Kazalika, ya shawarci masu mutane masu mu’amala da Musulmi da su guji ketara iyakarsu, domin “Muna da wata iyaka ba a tsallakawa.”
Ya jadadda cewa Annabi Muhammad (SAW) na daga cikin na gaba-gaba daga abubuwan da ba a tabawa a kwana lafiya a addinin Musulunci.
Frafesa Maqari, ya ce bai dace mutane su mayar da hankalinsu kan mutuwar Deborah kadai ba.
Akwai bukatar yin duba ga abin da ta aikata wanda shi ne ya jawo abin da ya faru da ita.