Batanci ga Annabi: Iran ta karrama matashin da ya kai wa Salman Rushdie hari

An karrama matashin ne saboda bajintar da ya nuna wajen neman ran marubucin da ya yi batanci ga Manzon Allah (SAW)

Batanci ga Annabi: Iran ta karrama matashin da ya kai wa Salman Rushdie hari

Salman Rushdie

Wata gidauniya a kasar Iran ta karrama matashin nan da ya kai hari ga marubucin nan da ya i batanci ga Manzon Allah (SAW), Salman Rushdie.

Gidauniyar mai bibiyar da kuma dabbaka fatawowin Imam Khomeini, ta karrama matashin ne saboda bajintar da ta ce ya nuna inda ta ba shi kyautar filin noma mai fadin mita 1,000.

A watan Agustan bara ne matashin wanda mabiyin Darikar Shi’a ne a Amurka ya kai wa Rushdie farmaki a wurin wani taro a birnin New York.

Harin ya yi sanadiyar Rushdie ya rasa idonsa daya, haka ma hannunsa daya ya daina aiki.

Harin na mazaunin aiwatar da fatawar da tsohon Shugaban Shi’a, Ayatollah Ruhollah Khomeini ya bayar ne na zartar wa Rushdie hukuncin kisa, shekaru 33 da suka gabata.

A wancan lokaci, Khomeini ya yi kira ga Musulmi da a kashe marubuci Rushdie saboda wani littafi da ya rubuta mai suna ‘The Satanic Verses’, wanda a cikin littafin ya yi batanci ga Manzon Allah (SAW).

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna