Batanci ga Annabi: Shugaban Turkiyya ya nemi a daina sayen kayan Faransa
Erdogan ya bukaci a yi wa Macron gwajin kwakwalwa saboda yadda yake adawa da Musulunci
A yayin da ake ci gaba da tsama tsakanin Faransa da Turkiyya kan tsangwama da kyamar addinin Islama, Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya nemi al’ummar kasarsa da su kaurace wa siyan duk wasu kayayyaki da suka fito daga kasar Faransa.
Shugaba Erdogan ya yi kiran ne ranar Litinin a birnin Ankara, yayin bude makon bikin Maulidin Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad (SAW).
- An yi artabu tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zangar Iraki
- Magidanta 4 sun amsa laifin aikata luwadi da kananan yara a Katsina
Yayin bayyana damuwa a kan yadda tsangwamar addinin Islama ke karuwa a nahiyyar Turai, ya kuma yi kira ga Shugabannin Tarayyar Turai da suka kawo karshen abin da ya kira wata manufar Shugaban Faransa ta da’awar kyamar musulunci da musulmi.
Cikin wani rahoto da BBC ta wallafa, akwai tsamin dangartaka tsakanin kasashen biyu, biyo bayan yadda Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya nuna adawarsa ga wani mai kishin addinin musulunci da ya fille kan wani malamin makaranta a watan da ya gabata saboda nuna wa dalibansa zanen barkwanci na Fiyayyen Halitta.
A makon da ya gabata, Erdogan ya bukaci Macron ya yi gwajin kwakwalwa saboda yadda yake tsabagen nuna adawa da addinin musulunci wanda hakan ya sanya Faransa ta janye jakadanta daga Turkiyya.