Batanci ga Annabi: Ya kone motarsa saboda kin Faransa
Hoton wani mutum da ke yawo a kafafen sada zumunta, ya nuna yadda ya kone motarsa kirar Peugeot domin ya nuna rashin kyamarsa ga kaya kirar kasar Faransa. Hotonan guda biyu da suka kare kafafen sada zumunta sun bayyana cewa mutumin dan kasar Mauritaniya ne, inda a hoto na farko aka hango shi yana daukar […]
Hoton wani mutum da ke yawo a kafafen sada zumunta, ya nuna yadda ya kone motarsa kirar Peugeot domin ya nuna rashin kyamarsa ga kaya kirar kasar Faransa.
Hotonan guda biyu da suka kare kafafen sada zumunta sun bayyana cewa mutumin dan kasar Mauritaniya ne, inda a hoto na farko aka hango shi yana daukar hoton motar daga nesa kafin ya kona, sai hoto na biyu da ya nuna motar tana ci da wuta.
Tuni dai al’umar Musulmi a fadin duniya ke ci gaba da yekuwar kaurace wa kayayyakin da ake kerawa a Faransa domin nuna bacin ransu ga goyon bayan da shugaban kasar, Emanuel Macron ya yi wa batanci da aka yi wa Annabi Muhammadu (SAW) a kasarsa.
Musulmi daga kasashen Musulmai sun yi zanga-zangar kin jinin Shugaba Macron, yayin da miliyoyin Musulmi ke ci gaba da amfani da kafafan sada zumunta wajen yekuwar kauracewa amfani ko saye da sayar da kayayyakin da aka kera a Faransa.
Daya daga ciki maudu’in da jama’a ke amfani da su Facebook wajen yin yekuwar shi ne #Boycott_French_Products wanda zuwa yanzu mutum sama da milliyan 6 ne suka yi amfani da shi a Facebook din.