Batanci: Malaman Kano sun yaba da sauya sunan ‘France Road’

Alaramommi sun bukaci Gwamnatin Jihar Kano ta yanke hulda da kasar Faransa.

Batanci: Malaman Kano sun yaba da sauya sunan ‘France Road’

Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano a lokacin da yake jagorantar wata addua

Malaman Islama a Jihar Kano sun tilasta gwamnatin jihar sauya sunan titin ‘France Road’ da ke birnin Kano zuwa ‘Madina Road’ saboada kalaman batanci da Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi ga Manzon Allah da addinin Musulunci.

Kungiyar alaramommi da wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun kuma bukaci Gwamnatin Jihar Kano ta yanke mu’amala da duk wani abu da ya shafi kasar Faransa.

Sakataren kungiyar alaramommin, Dakta Saidu Ahmad Dukawa, bayan  taronsu a Masallacin Al-furqan a ranar Lahadi ya kuma kirayi gwamnatin Kano ta cire harshen Faransanci daga jerin harsunan da za ake koyarwa a makarantun jihar.

Alaramommin sun kuma cimma matsaya cewa Musulmi su ci gaba da nuna kiyayya ga Macron da duk wani abu da ya shafi kasarsa ta Faransa.

Sun kara da kira ga Musulmi su ci gaba da addu’o’in la’anta da tabewa ga Macron da daukacin masu goya masa baya.

Malaman sun kuma ankarar da Musulmin duniya cewa hakki ne da ya rayata a kansu kare kima da darajar Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.

Daga karshe kungiyar ta jinjina wa shugabanin da suka fito suka la’anci kalaman batancin da Macron ya yi.

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta