Batanci: Shari’ar Musulumci ta saba dokar kasa —Yahaya Sharif

Mawakin da kotun Musulunci ta kama da laifin batanci ga Annabi ya kalubalanci hukuncin

Batanci: Shari’ar Musulumci ta saba dokar kasa —Yahaya Sharif

Wadume: Kotu da dage sauraron shari’ar kisa

Wani matashi da Babbar Kotun Shari’ar Musulumci ta yanke wa hukunci kisa saboda batanci ga Manzon Allah (SAW) ya ce tsarin Shari’ar Musulumci a Jihar Kano ya saba wa tsarin mulkin dimokuradiyya da tsarin kundin mulkin kasa.

A lokacin da ya daukaka kara, a ranar Alhamis 3 ga watan Satumba, kan hukuncin da kotun Musuluci ta yanke masa, Aminu Yahaya Shariff ya ce tsarin Shari’ar Musulunci a Jihar Kano ya saba wa  tsarin dokar kasa da mulkin dimokradiyya.

“Tsarin Shari’ar Musulumci na faruwa ne a kasashen Musulumci ko kuma Daular Musulumci amma ba a kasa irin Najeriya da ba ruwanta da addini ba; domin dokar da ke kundin tsarin mulkin kasa da na demokuradiyya shi ne gaba da kowace irin doka”, kamar yadda yake a takardar daukaka karar.

A takardar daukaka karar shari’ar da matashin ya yi mai lamba CR/43/2020 ta hannun lauyansa Kola Alappini, ya yi karar Babban Alkalin Jihar Kano, tare da Gwamnan Jihar.

Daukaka karar na dogaro ne da cewa hukuncin kisa ta hanyar rataya da aka yanke wa mawakin ba ta bisa ka’ida saboda a cewarsa, tsarin Shari’ar  Musulunci da aka yanke wa mawakin hukuncin da shi ya saba ka’ida da kuma dokar kasa.

A cewar takardar daukaka karar, hukuncin kisan da aka yanke wa Aminu ya saba dokar Penal Code ta Jihar Kano ta 2000, da kundin mulkin Najeriya na 1999, da kuma usulin kare hakkin dan Adam na  kasashen Afirka da na duniya baki daya.

Ya ce tuhumar da ake masa na yin batanci ga Annabi (SAW) ba ta da tushe domin babu irin wannan laifin a tsarin mulkin Najeriya.

“Tsarin Shari’ar Musulumci na faruwa ne a kasashen Musulumci ko kuma Daular Musulumci amma ba a kasa irin Najeriya da babu ruwanta da addini; saboda dokar da ke kundin tsarin mulkin kasa da na dimokuradiyya shi ne gaba da kowace irin doka”, inji takardar daukaka karar.

Mawakin ya kara da cewa ba a ba shi damar jin ta bakinsa ba, kuma an yi shari’ar ne a boye, ta hanyar tauye masa hakkin jin ta bakinsa, tare da hana shi damar samun lauyan da zai kare shi.

“Gwamnatin Jihar Kano a matsayinta na sashen masu gabatar da kara ta gaza samar da tsaro ga mutanen da babu ruwansu da addini ko kuma mutanen da ke da wani addini na daban ko wasu kabilu’

“Ta haka ne take goya wa masu tsaurin ra’ayin addini baya, take kuma daure wa masu ta da tsaye da ’yan daba gindi domin nuna goyon bayanta ga al’ummar Musulmi”, inji shi.

Ya kara da cewa an gina Jihar Kano ne bisa tsarin kundin mulkin kasa don haka ba ta da hurumin yin doka a wani tsarin na daban da ya saba wa tsarin mulkin kasa.

A karshe mawakin ya bukaci kotun da ya daukaka karar ta soke tuhumar da ake masa da hukuncin da kotun Musulimcin ta yanke masa, kuma a yi masa adalci.

Tun da fari dai Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce a shirye yake ya sanya hannu a takardar hukuncin kisan da aka yanke wa mawakin da zarar wa’adin kwana 30 da aka ba shi ya daukaka kara sun cika.

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano

Ya kamata a kori shugaban INEC —Obasanjo