batancin da ake yi wa Buhari na kara masa karbuwa – Kwapnoe

Mista Aled Yola Kwapnoe shi ne ko’odinetan yakin neman zaben dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari a Jihar Filato. Tsohon dan Majalisar Dokokin Jihar ne daga Shendam kuma ya taba zama Kwamishina a jihar. A tattaunawarsa da wakilinmu ya ce batancin da ake yi wa Janar Buhari na kara masa […]

batancin da ake yi wa Buhari na kara masa karbuwa – Kwapnoe
batancin da ake yi wa Buhari na kara masa karbuwa – Kwapnoe

Mista Aled Yola Kwapnoe shi ne ko’odinetan yakin neman zaben dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari a Jihar Filato. Tsohon dan Majalisar Dokokin Jihar ne daga Shendam kuma ya taba zama Kwamishina a jihar. A tattaunawarsa da wakilinmu ya ce batancin da ake yi wa Janar Buhari na kara masa karbuwa a wurin al’ummar Najeriya:

Aminiya: Me za ka ce kan irin batancin da Jam’iyyar PDP da jami’an gwamnatin Jonathan ke yi kan dan takararku Janar Buhari?
Aled Kwapnoe: Wannan batanci da suke yi kan Janar Buhari aikin banza ne suke yi. Sun rikice ne kawai ya sa suke ta wannan batanci. Misali kamar maganar da suke yi cewa wai Janar Buhari ya tsufa. A lokacin da Cif Obafemi Awolawo da Cif Azikiwe suka yi takarar shugabancin kasar nan a Jamhuriya ta Biyu, dukkansu sun haura shekara 70. Haka a lokacin da Nalson Mandela ya tsaya takarar shugabancin kasar Afirka ta Kudu yana shekara 74 ne a duniya. A yanzu shugaban kasar Zimbabwe ya kai shekara 91, kuma har yanzu shi ne shugaban kasar. Wannan batanci da suke yi yana karfafa al’ummar Najeriya ne wajen son Janar Buhari. Don haka su ci gaba da yi, domin suna yi ne mu kuma muna ta dada samun karuwa.
Kuma ka dubi wani karin faduwa a gare su, a nan kan irin zagin da matar Goodluck Jonathan ta yi wa al’ummar Arewa. Kan wannan zagi da ta yi wa al’ummar Arewa idan ba munafiki ba, babu wani mutumin kirki daga Arewa da zai jefa wa Jonathan kuri’a.
Aminiya: To, me kake ganin ya sanya Jam’iyyar PDP ba ta son a yi amfani da na’urar tantance masu zabe a zaben da za a yi?
Aled Kwapnoe: Sun saba rubuta sakamakon zabe ne ba tare da an yi zaben ba. Ganin wannan na’ura ta hana wannan magudi da suka saba yi, shi ne ya sanya suke nuna rashin amincewarsu. Don haka suka rikice suke cewa ba su amince a yi amfani da na’urar ba.
Aminiya: Kana ganin za ku samu nasara a wannan zabe da za a yi?
Aled Kwapnoe: Da yardar Allah mun riga mun samu nasara a wannan zabe da za a yi. Babu yadda PDP za ta iya kayar da APC a wannan zabe da za a yi.
Aminiya: Idan muka dawo ga Filato yaya karbuwar Janar Buhari take a jihar?
Aled Kwapnoe: Ai tunda Janar Muhammadu Buhari yake fitowa takarar Shugaban kasar nan, bai taba samun karbuwa irin yadda ya samu a wannan lokaci ba a Jihar Filato. Domin a yanzu muna tare da manyan ’yan siyasar jihar nan da sauran al’ummar jihar nan a wannan tafiya.
Sai dai babbar damuwarmu kan wannan tafiya ita ce daga can Abuja wato sakatariyar wannan tafiya, ba sa taimaka mana kamar yadda ake taimaka wa sauran jihohin kasar nan, domin suna ganin kamar yadda wannan tafiya take a da haka take a yanzu. Mu ne da kanmu muke wannan kokari ba tare da samun wani taimako ba.
Aminiya: To, me za ka ce kan maganar da ake yi cewa Janar Buhari ba zai ci zabe a Jihar Filato ba, domin ana ganin kamar jiha ce ta PDP?
Aled Kwapnoe: Kamar yadda na fada maka dukkan fitattun mutanen jihar nan da sauran al’ummar jihar nan, suna tare da tafiyar APC. Domin wannan lokaci ne na canji, kuma babu wanda zai kawo mana wannan canji sai Jam’iyyar APC. Don haka dole ne APC ta samu nasara a Jihar Filato, in dai jama’a ke zabe. Domin gwamnatin Jang a cikin shekara 8 da ta yi tana mulkin jihar, ta jefa mu a cikin rikice-rikice da suka yi sanadin asarar dubban rayukan jama’ar jihar tare da asarar dukiya ta biliyoyin Naira.
Har ila yau gwamnatin Jang ta jefa jihar a cikin bashin kudi na sama da Naira biliyan 400 da za ta tafi ta bari. Wadannan bassusuka sun hada da bashin da ma’aikata da ’yan fansho suke bi da kuma bashin da ta ciwo a bankuna a nan gida Najeriya da kasashen waje. Har ila yau gwamnatin Jang ta rike wa al’ummar jihar nan kudaden rage radadin talauci na SURE-P Naira biliyan 80 da ta karbo daga Gwamnatin Tarayya, ba ta yi bayani kan inda ta kai wadannan kudade ba.
Kazalika wannan gwamnati ta Jang gwamnati ce da Gwamna ya dauki dan uwansa ya nada shi a matsayin babban sarki a jihar, ya dauki dan cikinsa ya nada kwamishina ya kuma sa shi a matsayin shugaban wasu ma’aikatun gwamnatin jihar har guda hudu. A yanzu yana neman Sanata kuma ya dauko ’yan uwansa guda biyu, daya ya tsayar da shi takarar Gwamnan Jihar, dayan kuma ya tsayar da shi takarar Majalisar Wakilai a Mazabar Jos ta Kudu da Jos ta Gabas. Don haka babu wanda zai dauki kuri’arsa ya bai wa wadannan mutane, domin yanzu mutanen jihar nan sun gane. Yanzu a jihar nan, duk inda ka shiga za ka ga kowa yana shara da tsintsiya.
Aminiya: To, wane sako ko kira ne kake da shi zuwa ga al’ummar Najeriya dangane da wannan zabe da za a gudanar?
Aled Kwapnoe: Sakona ga al’ummar Najeriya shi ne lokaci ya zo da ya kamata mu yi canji a Najeriya. Don haka mu fito kwanmu da kwarkwatarmu a lokacin wannan zabe, mu zabi wannan canji da kuri’unmu. Kuma kada wani ya zuga mu mu tayar da zaune-tsaye, musamman a nan Arewa, inda muke fama da matsalolin talauci da fatara.