Batun auren Rainbow da Rahama: Da sauran rina a kaba
A makon da ya gabata ne Aminiya ta kawo muku labarin yadda aka kasa gane inda batun auren fitaccen dan kasuwar fina-finan Hausa, Sani Rainbow da kuma jaruma Rahama Hassan ya dosa, kasancewar dan kasuwar ya ki yin gamsasshen bayani game da batun auren.Bayan fitar labarin ne sai wani shakikin dan kasuwar wanda ya nemi […]
OLYMPUS DIGITAL CAMERA

A makon da ya gabata ne Aminiya ta kawo muku labarin yadda aka kasa gane inda batun auren fitaccen dan kasuwar fina-finan Hausa, Sani Rainbow da kuma jaruma Rahama Hassan ya dosa, kasancewar dan kasuwar ya ki yin gamsasshen bayani game da batun auren.
Bayan fitar labarin ne sai wani shakikin dan kasuwar wanda ya nemi a sakaya sunansa ya gana da ‘yan jarida ciki har da wakilinmu, inda ya warware mana zare da abawa kan batun aure.
Ya ce, shi ne babban abokin Sani Rainbow, kuma babu abin da zai taso na Rainbow ba tare da ya yi ruwa da tsaki a ciki ba. “Amma ina tabbatar muku mutane ne kawai suke surutunsu. Har yau ba mu taba zama da Sani ya kawo mana labarin wai zai auri Rahama ba. Ban ce babu soyayya ba, domin ai mutane ne, amma idan har akwai tunanin aure a zuciyar Rahama, to babu shi a zuciyar Sani. Kun taba jin ya ce wani abu game da maganar a wata kafar yada labarai?”
Ya ce batun matarsa da ‘yan uwansa sun hana auren duk karya ne, domin kamar Sani a ce ba ya iya zaben matar aure sai da izinin wani, kuma har sai matarsa ta yarda? A gaskiya ba mu san da wata maganar aure tsakanin Rahama da Sani ba.”
Da Wakilinmu ya sake tambayar abokin Rainbow, ko yana sane da cewa hirar da Mujallar Fim ta yi da Rahama a gaban Sani aka yi ta, kuma bai nuna wata damuwa ba? Sai ya ce, “To ai abin da mutane ba su gane ba shi ne, akwai girmamawa a tsakaninsu, ba zai taba hana Rahama yin wani abu na soyayyar da take yi masa ba. Ai a wancan lokacin aikin fim dinsa ake yi mai suna ‘Hanyar Kano’, wanda aka yi a Kaduna, a nan suka hadu. To irin wannan girmamawar da ke tsakanin su ita ta jawo har aka dauke su wancan hoton da wasu ke dauka kamar na biki ne.”
Me zai ce duk da cewa an sanya hoton a shafin Facebook, sai ya ce, ya san da hoton, kuma tabbas zai sa a yarda da batun auren, amma a gane, su makusanta Sani sun yi bincike game da wannan hoton, sun kuma gano ba Rahama ba ce ta sanya shi. “Na biyu kuma an dauki hoton a wajen fitar da hotunan fostar wani fim ne. Rahama da Sani sun shaku fiye da yadda ake zato, shi ya sa har a wancan lokacin aka yi wannan hoton. Amma ba wai hoto ne na soyayya ba.” Inji shi.
Ina batun Rahama ta daina fim don zancen aurenta da Rainbow sai ya ce: “To ai ba Sani ya hana ta fim ba, a hirarta da Mujallar Fim ta ce ita ta ba kanta shawara cewa ya kamata ta daina fim don ta sa zancen aurenta a gaba.”
Batun wannan aure har yanzu da sauran rina a kaba, kasancewar Rainbow ya ki cewa komai. Kodayake lokaci ne kawai zai tabbatar mana gaskiyar al’amari.