Batun hijabi: Majalisar Malama ta yaba wa Buhari
Shugaban Majalisar Limamai da Malaman Addinin Musulunci ta Jihar Kaduna, Sheikh Abubakar Usman Babantune ya yaba wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan gaggawar janye cewa zai hana sanya hijabi a kasar nan. Majalisar ta ce dole ne a yaba wa Shugaban kasar kan jin koke-koken wadanda yake shugabanta.Shugaba Muhammadu Buhari a makon jiya lokacin […]
Shugaban Majalisar Limamai da Malaman Addinin Musulunci ta Jihar Kaduna, Sheikh Abubakar Usman Babantune ya yaba wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan gaggawar janye cewa zai hana sanya hijabi a kasar nan. Majalisar ta ce dole ne a yaba wa Shugaban kasar kan jin koke-koken wadanda yake shugabanta.
Shugaba Muhammadu Buhari a makon jiya lokacin tattaunawar musamman da manema labarai ya ce idan har hare-haren kunar bakin wake da ’yan Boko Haram ke kaiwa suka ci gaba za a iya hana sanya hijabi a kasar nan. Wannan magana ce ta sa al’ummar Musulmi ba su ji dadi ba, inda kungiyoyin Musulmi da malaman addini suka dirar wa Gwamnatin Tarayya suna neman a janye wannan shiri tunda wuri.
Fadar Shugaban kasa ta fitar da wata sanarwa dauke da sa hannun Kakakin Shugaban kasa, Malam Garba Shehu inda ta nuna an jahilci maganar Shugaba Buhari a kan zancen.
Ya ce babu yadda za a yi Shugaban kasa ya yanke irin wannan hukunci da ya shafi rayuwa da addinin jama’a ba tare da ya tattauna da masu ruwa da tsaki a kan zancen ba.
Sheikh Babantune ya ce akwai bukatar shugabanni su rika yin tunani kafin su rika fitar da zance musamman da ya shafi addinin ga jama’a. “Alal hakika janye wannan zance da Shugaban kasa ya yi ya cancanci yabo kuma ya cancanci a jinjina masa kuma haka ake bukatar shugaba ya zama, wato ya lura da abin da zai amfani al’ummarsa,” inji shi.
Ya kara da cewa: “Hadarin da muka duba dangane da matakin da ya so dauka shi ne a Najeriya muke idan muka yarda da abin da Buhari ya yi, nan gaba ana iya samun wani shugaba da ba Musulmi ba idan ya zo ya ce zai yi mana haka, in muka ce ba mu yarda ba daga nan rikicin addini na iya tashi. Akwai asarori a cikin abin, saboda haka mun yi matukar farin ciki muna godiya ga Shugaban kasa kuma majalisar za ta rubuta wasika domin nuna murnarmu gare shi dangane da ba shi nasiha da kuma daukar wannan nasiha da ya yi.”
Game da ina mafita idan aka ci gaba da kai hari ta amfani da hijabi, sai Sheikh Babantune ya ce akwai Majalisar Fatwa ta kasa da ta kunshi manyan malaman kasar nan, kuma ga Majalisar koli ta Addinin Musulunci da kuma Jama’atu Nasril Islam da Sarkin Musulmi ke jagoranta sai Gwamnatin Tarayya ta nemi shawararsu domin samar da mafita. “Sheikh Ibrahim Saleh Maiduguri ne Shugaban Majalisar Fatawar, Sheikh dahiru Usman Bauchi da Sheikh karibullah Nasiru Kabara da Sheikh Sani Yahaya Jingir da Sheikh Bala Lau da ni kaina da sauran manyan malaman kasar nan har da na Yarbawa suna cikin Majalisar Fatawar. Idan irin haka ya faru sai a tura masu akwai abin da malamai idan suka duba suna iya cewa ga abin da ya kamata a yi. Saboda haka nake jan hankalin Gwamnatin Tarayya da na jihohi musamman Jihar Kaduna cewa a duk lokacin al’amari ya taso irin haka da ya shafi addini a rika tura shi inda ya kamata su ba su fatawa domin kauce wa janyo kace-nace,” inji shi.