Batun karancin man fetur a kasar nan

karancin man fetur ba sabon abu ba ne a kasar nan, kasa ta 5 mafi fitar man fetur a duniya, amma dogayen layuka a gidajen mai kusan makonni biyu da suka gabata abin daure kai ne. Ababen hawan da suka yi dogayen layuka na tsawon wadansu kilomita a gidajen mai ya tabbatar da akwai gagarumar […]

Batun karancin man fetur a kasar nan
Batun karancin man fetur a kasar nan

karancin man fetur ba sabon abu ba ne a kasar nan, kasa ta 5 mafi fitar man fetur a duniya, amma dogayen layuka a gidajen mai kusan makonni biyu da suka gabata abin daure kai ne. Ababen hawan da suka yi dogayen layuka na tsawon wadansu kilomita a gidajen mai ya tabbatar da akwai gagarumar matsalar a tattare da yadda ake rarraba mai a Najeriya da kuma rashin tabbas a kan masana’antar mai a kasar nan. Hakan ya sanya ’yan bunburutu suka rika cin karensu babu babbaka, inda suka rika sayar da lita daya daga Naira 150 zuwa 250, duk da cewa gwamnati ta kayyade a sayar da kowace lita a kan Naira 85.

A lokacin da karancin mai ya ta’azzara sai Hukumar da ke kayyade Farashin Mai (PPPRA) ta sanar da cewa za ta kara shigo da miliyoyin lita na mai don cike gibin man da ake samu a kasar nan. Amma Ma’aikatar Man fetur ta bayyana akwai isasshen mai har zuwa karshen watan Maris, sannan ta zargi ’yan kasuwa da boye mai don wani dalili na kashin kansu.
kungiyar ma’aikatan masu hakar man fetur da kuma gas (NUPENG) ta yi zargin gwamnati ce ummul’aba’isin karancin mai a kasar nan, kasancewar ta ki biyan ’yan kasuwa bashin kudin da suka shigo da mai a lokutan baya.
’Yan kasuwar sun ce a yanzu faduwa suke yi wajen shigo da mai kasar nan sakamakon faduwar darajar Naira. Sun kuma koka cewa dalilin basussukan da ake binsu bankuna sun ki ba su shaidar amincewa (Letters of credit). Ita kuma jam’iyya mai mulki PDP ta ce jam’iyyar adawa ta APC ce ta kitsa karancin mai don a shafa wa gwamnati bakin fenti.
Ministar Kudi Dokta Ngozi Okonjo-Iweala ta ce a wani yunkuri na kawo karshen karancin mai a kasar nan ne, gwamnati ta ba ’yan kasuwa Naira biliyan 30 sakamakon asarar da suka yi dalilin faduwar darajar Naira, an bada wannan kudin ne bayan Naira biliyan 185 da aka bayar don biyan bashin da ake bin ’yan kasuwar.
Gwamnan Babban Bankin Najeriya Mista Godwin Emefiele ya ce, ya gana da bankuna da kuma ’yan kasuwar mai don warware duk matsalar da ta shafi basussuka a harkar shigo da mai kasar nan.
Duk wadannan abubuwa da suka faru sun nuna har yanzu ba a koyi darasi dangane da karancin mai da ake samu a kasar nan ba, duk da cewa ana samar da gangar danyen mai miliyan 2.2 kowace rana a Najeriya, har yanzu ba a iya tace danyen mai a kasar nan, inda da an yi hakan za a samu sassauci.
Abin takaicin shi ne, Najeriya ce kadai mambar kungiyar kasashen da ke samar da mai (OPEC) amma ke shigo da man da take amfani da shi daga wata kasa, ta kuma gaza magance karancin mai da ake fuskanta a kasar nan.
Ya zama dole a kawar da matsalar karancin mai gaba daya a kasar nan. A shekarar 2012 gwamnati ta sa hannu a wata yarjejeniya da wadansu kamfanoni na kasar China don gina matatar mai uku, har yanzu ba a san ina kwanan zancen ba. Haka kuma a shekarar 2012 an amince da kwangilar Dala biliyan 4.5 don gina kananan matatun mai a kasar nan, wadanda za su rika samar da gangar danyen mai dubu 180 kowace rana, amma har yanzu ba san inda aka tsaya ba.
Don haka batun za a kawo karshen wannan al’amarin bisa matakan da aka dauka a yanzu ba mai yiwuwa ba ne, musamman da Ministar Man Fetur, Diezani Alison-Madueke ta bayyana kasashen Afirka za su ci gaba da shigo da mai har zuwa nan da shekara 20, ko da kuwa an gina matatun mai da suke aiki. Ta jaddada ko an gina matatun mai ba za su kawo karshen karancin mai a Najeriya ba.
A lokacin da Shugaba Goodluck Jonathan yake jawabi a kan karancin mai, ya ce, hanya daya da za a bi don magance wannan matsalar ita ce, idan matatun mai a kasar nan suka fara aiki. Abin tambayar shi ne, me ya sa matatun ba sa aiki? Kada a manta wannan gwamnati tana ci gaba da ba ’yan siyasa da shalele lasisin shigo da mai kasar nan. Dole sai an rufe ido an hana masu shigo da mai kasar nan, wanda zai yi wahala a iya hakan.
Idan ba a dauki matakin da ya dace ba, to nan gaba kadan karancin mai zai sake dawowa, don haka dole a zauna a sake duba matsalolin da suke haifar da karancin mai, sannan a fito da hanyoyin magance su, don a huta da kawar da matsalar gaba daya.