Batun karin albashi ya zo a kan kari
Assalamu alaikum. Editan Aminiya. Batun karin albashi ya zo a kan kari, kuma tallafin kyautata rayuwa ne da ya dace a yi wa ma’aikatan kasar nan tuntuni. Ko shakka babu shirin nazarin karin albashin da Gwamnatin Tarayyar Najeriya karkashin jagorancin Shugaba Buhari ke shirin yi, wannan ya yi daidai, kuma Allah Ya sa hakan ya […]
Assalamu alaikum. Editan Aminiya. Batun karin albashi ya zo a kan kari, kuma tallafin kyautata rayuwa ne da ya dace a yi wa ma’aikatan kasar nan tuntuni. Ko shakka babu shirin nazarin karin albashin da Gwamnatin Tarayyar Najeriya karkashin jagorancin Shugaba Buhari ke shirin yi, wannan ya yi daidai, kuma Allah Ya sa hakan ya kasance.
Domin haka shi ne zai rage yawan wahalhalun da mutane suke ciki. A yi duba zuwa ga yadda kayan masarufi suka yi tashin gauron zabbi, kuma har zuwa yanzu wasu daga cikin kananan ma’aikata suna karbar albashin (18,000), to wannan albashin ba zai wadace su ba.
Ganin irin yadda komai a kasar nan yake da tsada, albashin da ake ba su wanda bai taka kara ya karya ba, wajen sayen kayan abinci ma, kudin ba zai isa ba, to ina ga al’amurran yau da kullum? Ko shakka babu muna alfahari da zamanka shugaban kasarmu Muhammadu Buhari. Domin a kullum burinka bai wuce talaka ya ji dadi ba.
Da wannan muke yi maka fatan alkhairi, kuma da addu’ar zaman lafiya ga yankin Arewa da ma kasa baki daya! Allah Ya kara daukaka Najeriyarmu, da jama’ar ta.
Daga Nura Muhanmad Mai Apple Gusau/ 08133376020 nura Muhammad Gusau <[email protected]>