Batun magance illolin likitocin bogi
A kwanan nan ne ’yan sanda suka bankado asirin wani likitan bogi da ya yi sojan gona, ya saci takardun shaidar abokinsa likita, ya samu aiki a Ma’aikatar Lafiya Ta Tarayya na kusan tsawon shekaru goma. Wannan abin takaici na yin ishara da yadda al’amuran ma’aikatar suka sukurkuce kuma hakan ke nuni da cewa Allah […]
A kwanan nan ne ’yan sanda suka bankado asirin wani likitan bogi da ya yi sojan gona, ya saci takardun shaidar abokinsa likita, ya samu aiki a Ma’aikatar Lafiya Ta Tarayya na kusan tsawon shekaru goma. Wannan abin takaici na yin ishara da yadda al’amuran ma’aikatar suka sukurkuce kuma hakan ke nuni da cewa Allah kadai Ya san adadin yawan bara-gurbi irinsa da suka dade suna aikata wannan ta’annati.
Kamar yadda rahotannin suka tabbatar, sunan likitan bogin Martins Ugwu kuma ya kasance babban jami’i a Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC), inda ya yi aiki tun daga 2006 da sunan bogi na Dr. George Dabidson Daniel har zuwa ranar da ’yan sanda suka rutsa da shi a Abuja.
Tun da farko dai kungiyar Lilitoci ta Najeriya ce ta fara yin kira da a kama likitan bogin, kasancewar a matsayinta na uwa ga daukacin likitocin da ke akwai a kasa, tun da ita ce ke yi musu rijista da kuma bin kadin ayyukansu. Hakan ya faru ne bayan da ta gudanar da bincike, inda ta gano cewa likitoci biyu mabambanta suna amfani da suna iri daya. Binciken ya samo asali ne da wata takardar koke da ta nemi a bi kadin Dr. George Dabidson Daniel da ke aiki a NCDC, inda aka gano cewa hoton da ke hannun kungiyar ya bambanta da mai sunan na ainahi. Haka jagoran binciken, Dr. Henry Okwuokenya ya bayyana.
“A lokacin da muka duba ma’ajiyarmu ta bayanai, mun gano cewa lallai akwai wani mutum mai suna Dr. George Dabidson Daniel amma kuma hoton ya bambanta da wanda aka aiko mana domin mu tantance,” inji shi.
Shi wannan Daniel na bogi, takardun da ke hannunsa ba orijina ba ne kuma lasisinsa na aikin likita na wucin gadi ne da ake bayarwa na tsawon shekara biyu kacal amma da muka tantance sai muka ga sunan da ke a rumbun bayananmu ya yi daidai da sunansa.
“Sahihin mutumin da ke da wannan sunan likita ne da ke aiki a Asibitin Koyarwa na Jos,” inji Okwuokenye.
Likitan na bogi, ya kwashe kusan shekaru goma yana aiki a karkashin Gwamnatin Tarayya kuma a Babban Birnin Tarayya, a karkashin Ministoci daban-daban na Hukumar Lafiya ta Tarayya, kuma a shi ne ma ke shugabantar Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najerya (NCDC).
Duk tsawon lokacin nan ya ci gaba da gudanar da aikinsa na bogi ba tare da asirinsa ya tonu ba, duk kuwa da cewa wai ana tantance ma’aikata, balle ma a 2010 ya rubuta jarabawar karin girma, har ma aka tura shi ya shiga layin masu mukamin daraktoci.
Inda Allah Ya taimaka ma shi ne, likitan bogin nan ba aikin asibiti yake gudanarwa ba kai tsaye, ya boye ne a Hukumar Lafiya, bangaren aikin ofis. Amma koma dai me ke nan, wadanda ke da alhakin kulawa ba su kula ba. Idan ba haka ba, yaya za a yi wannan sakacin ya faru? Ai da masu kulawa na gudanar da aikinsu yadda ya kamata, da tun daga watanni shida na farkon shiga aikinsa ya kamata a ce asirinsa ya tonu, tun da kowane ma’aikaci ana kiwonsa ne na tsawon wata shida kafin tabbatar da shi ya zama cikakken ma’aikaci.
Batun ma’aikatan jabu ba ga likitoci kadai ya tsaya ba, domin kuwa a kasar nan ana samun jabun lauyoyi, jabun injiniyoyi, jabun ’yan jarida, jabun ’yan sanda da sojoji, har ma da jabun farfesoshi. Wani abin mamaki ma, jabun Farfesa ya fi saurin samun aiki fiye da direban mota. Idan za a dauki direba aiki sai an tantance kwarewarsa sosai, amma mutum da jabun takardun shaida za a iya daukarsa aiki a matsayin Farfesa!
Wannan abin da ya faru ya kamata ya bude idon gwamnati da cibiyoyin daukar ma’aikata na kowane mataki, su shigo da tsare-tsare masu inganci yadda za a iya tantance sahihan takardun shaida daga na jabu. A wannan zamanin, mutane na kawo takardun shaidu na bogi daga jami’o’in kasar waje kuma ba a tantancewa ma a gano ko akwai makarantar ko babu. Sai ka ga an ba irin wadannan mutane gurbin aiki mai tsoka, alhali mai sahihan takardun ma bai samu ba.
Ya kamata a tashi tsaye a tsarkake ma’aikatu daga illar bara-gurbin ma’aikata. kungiyoyin ma’aikata kamar lauyoyi da injiniyoyi da sauransu, ya kamata su fito da wani tambari ya ka junansu, ta yadda za a iya tantance mai kyau daga bogi. Kamata ya yi duk wanda aka kama da laifin sojan gona, a hukunta shi sosai ta yadda zai zama darasi abin misali ga na gaba.