Batun malaman makaranta dubu 20 na Kaduna

Hakika abin takaici ne matuka game da sanarwar da Gwamnatin Jihar Kaduna ta fitar a kwanan nan cewa, malaman makarantun furamare dubu 21 da 780 cikin malamai dubu 33 sun gaza lashe jarabawar da aka shirya ma su ta matakin ‘yan aji hudu na furamare don tantance cancantar su. Sanarwar hakan ta fito ne daga […]

Batun malaman makaranta dubu 20 na Kaduna

Hakika abin takaici ne matuka game da sanarwar da Gwamnatin Jihar Kaduna ta fitar a kwanan nan cewa, malaman makarantun furamare dubu 21 da 780 cikin malamai dubu 33 sun gaza lashe jarabawar da aka shirya ma su ta matakin ‘yan aji hudu na furamare don tantance cancantar su. Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin gwamnan jihar, Malam Nasir El-rufai a tsakiyar wannan watan, a lokacin da ya karbi bakuncin Tawagar Babban Bankin Duniya a Kaduna.

Gwamnan ya ce, “Mun jarraba malaman makarantun furamare dubu 33 ta hanyar ba su jarrabawar ‘yan aji hudu na furamare. An yi tsammanin cewa za samu a kalla maki 75 cikin 100 na jarrabawar amma sabanin haka, ina mai bakin cikin sanar da cewa kashi 66 cikin 100 na malaman ba su samu wannan makin ba.”

Gwamna El-rufai ya kara da cewa jihar ta na shirin daukar sababbin ma’aikata dubu 25 a kokarinta na inganta harkar ilimi a jihar. “dauko hayar malaman makaranta da aka yi a baya siyasa ce kawai, amma muna da bukatar sake inganta fasalin ilimin ta hanyar shigo da matasan malaman makaranta kuma nagartattu wadanda za su daukaka ilimi zuwa matakin da ya dace a jihar nan.”

Abubuwa da dama ya kamata a kalla game da wannan batu na faduwar malaman makarantar kasa wanwar, ba ma a Jihar Kaduna ba a kasa baki daya. Da farko akwai karancin horo da malaman kan rasa a kusan dukkan matakan ilimin koyarwa a kasar nan. Haka kuma ayyukan kula da malaman ‘superbision’ ya yi batar dabo a dukkan makarantunmu don tada komadar ilimin na furamare. Sannan kuma da rashin karsashi da zumudin karantarwar ga su malaman. 

Domin a yau babu wani abin sha’awa ko daukar hankalin marasa aikin yi da karantarwa ke da shi tsawon shekaru, domin mafi yawan kwararrun malaman da suka samu kyakkyawan horo suna gujewa aikin karantarwar zuwa ga wasu ayyukan masu gwabi, yayin da aka bar bara-gurbin malaman cikin harkar karantarwa baki daya.  

Wannan shelar da Gwamna Nasir El-rufai ya yi ta daukar sababbin malamai dubu 25 don maye gurbin wadanda ba su cancanci karantarwar ba, ta janyo suka da cece ku ce mai yawan gaske ga gwamnatin jihar. Duba da fuskokin biyu, ya na da matukar amfani a fahimci manufar matsayar da gwamnan ya dauka kan lamarin. Akwai wadansu muhimman abubuwa guda uku wadanda ke nuni da matukar bukatar gogaggu kuma kwararrun malamai. A kullum akwai bukatar zakakurin malami ya san kyawawan hanyoyin isar da sakon ilimi ga wadanda yake karantarwa cikin sauki, kamar yadda ake bukatar ya rika sanin matakin ilimin dalibansa ta yadda zai rika dora mu su darussan mataki-mataki. Amma abu mafi a’ala ga dukkan wadannan matakan biyu shi ne sanin ilimin kansa da kuma darasin kansa.

Tare da kwararren malami kuma mai nagarta za a iya samun nasarar nagartaccen ilimi ko da kuwa koyarwar na gudana ne a karkashin itaciya. A daya bangaren kuma, babu wani ingantaccen ilimin da za a cimma nasarar samunsa koda kuwa cikin kawatattun azuzuwa tare da dukkan kayayyakin karantarwa matukar malamin fanko ne wanda bai cancanta ba, don haka a maimakon daga ilimin sama sai a rusa shi baki daya. 

Dukkan malamin da za a ce ya gaza cin kwatankwacin jarabawar daliban da yake karantarwa, to ya yi hannun riga da asalin ma’anar malanta da kuma hakikanin darussan karantarwa baki daya, ba ma haka ba, bai dace ya ci gaba da amsa sunan malami ba sam. Don haka yunkurin Gwamna El-rufai na korar baragurbin malaman makarantar furamaren da suka fadi jarabawar sannan ya maye gurbinsu da nagartattu wadanda za su iya aikin, abin dubawa ne. Amma duk da hakan akwai bukatar gwamnan ya sake yin la’akari da korar adadin malamai ma su yawa irin wannan.

Kila korar malaman makaranta har kimanin budu 20 sai ya fi zama matsala fiye da barin malaman da aka gada marasa nagarta da sanin makamar aikin. Sannan babu tabbacin cewa malaman da za a dauka su maye gurbin wadancan din za su iya kai banten su, kasancewar dukkan su daga uwa guda suka tsotsi nono. Saboda abu ne mai matukar wuya a iya samun adadin kwararrun malamai har dubu 25 wadanda suka cancanta a lokaci guda.

Don haka wannan babban abin takaici na faduwar malaman za a iya shawo kansa muddin an dauki matakan da suka dace. Dole ne a rika shirya tarukan horaswa a matakin jiha da kananan hukumomi don inganta ilimin malaman da abun ya shafa. Haka kuma ya kamata jihar ta yi hadin gwiwa da Cibiyar Horas da Malamai ta kasa (NTI), sannan kuma Kwalejin Ilimi ko tsangayar ilimi a jami’ar jihar su rika shirya samina da tarukan kara wa juna sani kan makamar aiki da ilimi. Bugu da kari karantar da malaman da suka fadi ya zama cikin azuzuwa kamar dalibai don tabbatar samun nasarar abin da ake so su iya cikin lokaci ya na da matukar muhimanci.