Batun rage radadin talauci tsakanin mata da matasa a Jihar Katsina

Malam Hassan Nagado, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum ya aiko mana da wannan tsokaci:Kamar yadda alkaluman kidayar jama’a ta 1996 ta nuna, Arewacin Najeriya na da yawan mutane sama da miliyan miliyan 76. Cikin wannan adadi, matasa ’yan shekara 25 su suke da kaso 70 cikin dari. Haka kuma masana a harkar tsimi […]

Batun rage radadin talauci tsakanin mata da matasa a Jihar Katsina

Malam Hassan Nagado, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum ya aiko mana da wannan tsokaci:
Kamar yadda alkaluman kidayar jama’a ta 1996 ta nuna, Arewacin Najeriya na da yawan mutane sama da miliyan miliyan 76. Cikin wannan adadi, matasa ’yan shekara 25 su suke da kaso 70 cikin dari. Haka kuma masana a harkar tsimi da tanadi sun tabbatar da cewa Arewa ita ce kashin baya a kasar nan ta fannin talauci da rashin aiki da rashin lafiya.
A yayin da sauran yankunan Najeriya ke kokarin ririta albarkatun da Allah Ya ba su wajen ganin sun ’yanta matasansu, sun sama masu abin yi kuma da bunkasa tattalin arzikinsu, a Arewa labarin ya sha bamban. Wannan ya haddasa karuwar zaman kashe wando ga matasa, ya haifar da tashe-tashen hankali da suka danganci kabilanci, addini, kbangaranci da sauransu, kamar kuma yadda ya sanya matasan suka zama tamkar wani makami da wasu ke amfani da shi wajen lalata masu rayuwa.
A Jihar Katsina, haka al’amarin yake, inda matasa suka zama marasa alkibla, marasa aikin yi, sai gararamba da zaman kashe wando har zuwa 2007. Kafin wannan shekara, an kiyasta cewa akwai matasa sama da miliyan daya da rabi wadanda ba su da aikin yi a Jihar Katsina. Mafi yawansu sun kammala karatun Kwalejin Kimiyya da Fasaha, wasu ma digiri gare su, a yayin da wasu sun kammala kwalejin ilimi amma babu aikin yi bare wata sana’ar da za ta sama masu abin saka wa bakin salati.
Irin wadannan matasa ne wasu karkatattun ’yan siyasa suka rika amfani da su wajen bangar siyasa. An rika amfani da su wajen yi wa abokan hamayyar siyasa barazana ko ma lahanta su a yayin zakbe ko wajen kamfe. Hatta jami’an tsaro, wannan al’amari ya sha masu kai, a yayin da iyaye kuwa suka rasa abin yi domin shawo kan lalacewar matasan.
Inda al’umma suka fara samun sa’ida, shi ne lokacin da Gwamnatin Gwamna Ibrahim Shema ta hau karagar mulkin jihar, inda nan take ta fara neman hanyar gina al’umma. Wannan ya sanya ta fara kafa kananan masana’antu, kamar na yin fenti, allin rubutu, takin zamani a Batsari da Mai’aduwa da Safana da Bakori. A 2009 ne ma aka kirikri sansanin koya wa matasa sana’o’in hannu, wanda a nan aka rika kyankyashe matasan da suka kware wajen sana’o’i da ayyukan hannu iri daban-daban da suka hada da gyaran wayar hannu, kirar tukwanen karfe, daukar hoto, shirya fim da sauransu da dama. A yayin yaye kowane dalibi, akan ba shi kayan aiki da kuma jarin da zai kama sana’ar kashin kansa. Haka kuma, ana ba su bashin kudi a matsayin jari, bashin da babu ruwa cikinsa kuma mai saukin biya. A duk shekara ana yaye dalibai 2000.
Ba matasa maza da mata masu lafiya ne kadai ake koya wa sana’a ba, domin kuwa shirin ya hada har da nakasassu, kamar guragu da sauransu. Cikin irin wadannan nakasassu, ana koya masu yadda ake kera sandunan wutar lantarki, yadda ake sarrafa karafan gini da sauran sana’o’in da za su iya yi da hannu. Wannan ya taimaka wajen rage barace-barace, sannan kuma ya zama wata hanya ta kara gina al’umma.
A wannan tsari na sama wa matasa da mata madogara a Jihar Katsina, domin magance radadin talauci da rashin aikin yi, an koya wa mata sama da 2000 aikin kurosha (farfasa dutse da na’ura). Wasu kuwa an koya masu sana’ar rini da saka da dinki. Wannan ya taimaka gaya wajen rage zaman kashe wando da dinbim matasan suka dade suna yi a jihar. Hakan kuma ya sanya matasan a yanzu suka bambanta da na sauran jihohi, wadanda ba su da irin wannan tsari, wanda dalili ke nan al’amuran bangar siyasa suka ragu sosai koma suka kawo karshe.
Al’adar nan ta ‘Alhaji sai ka dawo’ da a can baya ta zama ruwan dare ga matasan Jihar Katsina ta zama tarihi a yanzu, saboda samuwar wannan tsari na koya wa mata da matasa sana’o’in hannu. Wannan al’ada na nufin yadda matasan kan zama masu maula da tumasanci ga mawadata.
Baya ga wannan tsari, gwamnatin kuma tana maida hankali wajen tsoma matasa a duk wani tsari da ta fito da shi. A kwana nan ne ma gwamnatin ta dauki matasa 500 daga kowace karamar hukuma domin aikin tsaftace muhalli, inda a kowane wata ake biyansu tukwicin Naira 5000.
An yi ittifakin cewa nan da ’yan shekaru, matasa ’yan Jihar Katsina da ake kyankyashewa daga sansanin koya sana’o’in hannu za su mamaye kowace irin sana’ar hannu da baki suka yi kaka gida a cikinta a jihar. Haka kuma za su bazu zuwa sauran jihohi da ma kasa baki daya. Wannan ke nuna irin yadda zaman kashe wando ya zama tarihi ga matasan.
Babu shakka wannan tsari abin yabawa ne, domin kuwa ya taimaka kuma zai ci gaba da taimakawa wajen sama wa matasa da mata madogara, sannan kuma ya taimaka wajen gina jihar da kasa baki daya. Lallai ya dace sauran jihohi su yi koyi da wannan tsari, domin ganin kasa gaba daya ta bunkasa, matasa sun zama masu dogaro da kansu.