Batun sanya hijabi a makarantun Jihar Osun
A makon jiya ne wadansu dalibai a makarantar Baptist High School a garin Owo na Jihar Osun suka je makarantar sanye da tufafi limaman addinin Kirista. Sun yi hakan ne don nuna adawa da hijabin da dalibai mata Musulmi suke sanyawa. Hakazalika, wadansu dalibai Kiristoci na makarantar Salbation Army Middle School da ke garin Alekuwodo […]
A makon jiya ne wadansu dalibai a makarantar Baptist High School a garin Owo na Jihar Osun suka je makarantar sanye da tufafi limaman addinin Kirista. Sun yi hakan ne don nuna adawa da hijabin da dalibai mata Musulmi suke sanyawa. Hakazalika, wadansu dalibai Kiristoci na makarantar Salbation Army Middle School da ke garin Alekuwodo a jihar, su ma sun kwoikwayi takwarorinsu na wancan makarantar. Duka wadannan makarantun gwamnati ne, kodayake, a da makarantun Mishan ne wadanda gwamnati ta karba a shekarar 1975.
Tun da farko, reshen kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) ta umarci dalibai Kiristoci da su sanya kayan zuwa coci idan za su je makaranta da zarar gwamnatin jihar ta fara aiki da hukuncin Babbar Kotun Jihar, wadda ta amincewa mata Musulmi sanya hijabi.
Matakin kamar yadda Shugaban kungiyar CAN a Jihar Elisha Ogundiya ya ce, an dauke shi ne lokacin wani taron gaggawa da kwamitin zartarwar kungiyar ya yi a garin Oshogbo. Kimanin makonni biyu da suka wuce ne Babbar Kotun ta sanye hukuncin cewa a kyale dalibai mata Musulmi su sanya hijabi a duka makarantun firamare da sakandaren mallakin gwamnatin jihar. Hukuncin kotun wanda Alkali Jide Falola ya yanke, ya ce daga yanzu duk wata muzgunawa ko tsangwama ko azabtarwa saboda dalibai Musulmi sun sanya hijabi za a dauki hakan a matsayin take musu hakkinsu na dan Adam, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar nan na shekarar 1999 ya bayyana.
A ranar 14 ga watan Fabrairun shekarar 2013 ne al’ummar Musulmin Jihar Osun ta shigar da kara a gaban kotun, tana bukatar a bar dalibai mata Musulmi su sanya hijabi a makarantun gwamnati. An yi karar gwamnatin jihar ne da kwamishinan ilimin jihar da kuma lauyan gwamnatin jihar. kungiyar CAN da kuma shugabanta a jihar bisa raddin kansu suka shigar da kansu batun. Wadanda suka shigar da karar a sakin layi na 44 na takardar karar, sun shaida wa kotun cewa dalibai mata Musulmi suna fuskantar tsangwama idan suka sanya hijabi, inda suke cewa wula ce kawai aka yarda dalibai su sanya a makarantun gwamnati.
A hukuncin da kotun ta yanke, Mai Shari’a Falola ya ce an shigo da batun addini ne cikin karar bayan da kungiyar CAN ta shiga karar. Ya ce ya yanke hukuncin ne bayan duk wani yunkuri warware takaddamar cikin ruwan sanyi ya ci tura. Reshen kungiyar CAN a Jihar ya bayyana aniyyarsa ta daukaka karar zuwa gaba. Daga nan kuma kungiyar ta shawarci gwamnatin jihar da kada ta fara aiki da hukuncin kotun, tare da yin barazanar idan ta yi hakan, za ta umarce dalibai Kiristoci da su sanya kayan limaman Kiristoci zuwa makaranta, wanda kuma hakan aka yi.
Gwamnan Jihar Rauf Aregbesola ya shawarci bangaren da hukuncin kotun bai yi wa dadi ba, da su yi amfani da matakan shari’a wajen bayyana rashin gamsuwarsu, madadin su ce za su dauki mataki da kansu. Ya ce akwai matakai daki-daki da shari’a ta tanada don bayyana rashin gamsuwarsu ga matakin babbar kotun. Kodayake, kungiyar CAN tana zargin gwamnan wanda Musulmi ne da kulla hukuncin kotun.
Sanya hijabi da dalibai mata Musulmi suke yi a makarantun gwamnati a yankin Arewa da Kudu-maso-Yamma ba sabon abu ba ne. Gwamnatoci a matakai daban-daban sun bai wa dalibai mata Musulmi zabi rufe kansu zuwa kirjinsu a kan tufafin makaranta da suke sanyawa. Haka yake a duka Kwalejojin Gwamnatin Tarayya da kuma Kwalejojin Fasaha mallakin Gwamnatin Tarayya, kamar yadda Ma’aikatar Kula da Ilimi ta Gwamnatin Tarayya (FME) ta amince da shi. dalibai mata Musulmi suna sanya hijabi a makarantun firamare da sakandare a jihohi da dama na kasar nan, kamar su: Sakkwato da Kaduna da Filato da Neja da Kwara da Bauchi da sauransu. Sai dai Ma’aikatar (FME) ba za ta iya tsoma baki a batun hijabin Jihar Osun din ba, saboda wannan hurumi ne na gwamnatin jihar.
Muna kira da reshen kungiyar CAN na Jihar Osun da ya fahimci batun, kuma su kasance masu yakana don ganin an warware matsalar cikin ruwan sanyi. Ya kamata mu kasance masu koya wa ’ya’yanmu dabi’u masu kyau, ba daidai ba ne mu koya musu bijirewa hukuma, inda za mu umarce su su sanya tufafin limaman coci su tafi makaranta. Har ila yau, muna kira ga ’yan siyasa da su guji amfani da addini wajen cimma muradun kashin kansu.