Batun Shigar Tsiraici: Jerangiyar batutuwa daga makaranta
A sakamakon maudu’inmu na makon jiya, makaranta sun antayo da sakonni daban-daban, don haka za mu dauki wasu daga ciki. FDK na kara tunatar da masu aiko da sako das u tabbatar sun sanya suna, adireshi da lambar waya a kasan sakonsu. Ga matan daba sa son a saka lambarsu, sai su sanar. Anas Nuhu […]
A sakamakon maudu’inmu na makon jiya, makaranta sun antayo da sakonni daban-daban, don haka za mu dauki wasu daga ciki. FDK na kara tunatar da masu aiko da sako das u tabbatar sun sanya suna, adireshi da lambar waya a kasan sakonsu. Ga matan daba sa son a saka lambarsu, sai su sanar.
Anas Nuhu Rijiyal Lemo (07034312244): Nuna tsaici ma ya wuce ga ’yan mata kawai, kai hatta masu auren ma suna yi, ganin yadda suke kai wa teloli samfuran dinkin da suke gani a fim ko a mujalla. Wanda kai tsaye za ka iya cewa an saki layin da addini ya ce mata su rufe tsiraici. Idan kai duba na tsanaki za ka yi wa kakanninmu murna, ta yadda suke rufe jikinsu ruf da tufafi, komai a wadace – riga doguwa, zani mai yalwa ba siket ba, hijabi kam har kasa ba gyale shara-shara ba. Wani abin mamaki mazan ma ba su kula mace mai nuna tsiraici, sai dai a yi hira ba dai maganar aure ba. FDK, ya kamata ’yan mata su game cewa wadatacciyar sutura ita ce ta fi dacewa da mata.
Sailuba Sulaiman Sheka-Kano (08146754240): Ina mika gaisuwata ga FDK, Allah Ya karbi ayyukanmu baki daya. Gaskiya na ji dadin wannan fadakarwa taka bisa ga yadda wannan dabi’a da ta yi yawa a cikin al’umma. Abin wallahi sai dai addu’a Allah Ya sa mata su yi amfani da wannan fadakarwa taka. Mun gode.
Sabi’u Nura Jihar Borno (08133388888): Ni bako ne a wannan filin. Babu shakka mace dukkanta al’aura ce kuma duk abin da aka ce al’aura ce, kai ma mai ita bai kamata ka kalla ba, balle wanda haram ne a gare shi. Za ka ja masa matsala kuma ka ja wa kanka. Allah Ka shirye mu albarkacin watan da muke ciki.
Isa A. Shani (08068636912): Barkanku da warhaka Malaman Dausayin Kauna. Hakika maudu’in wannan makon abin dubawa ne, Allah Ya sa mu gane.
Safiyanu S. Nuhu Kano, Sardaunan Masoya (08082262381): FDK, barka da shan ruwa da fatan Allah Ya karbi ibadarmu. Gaskiya ka taba min inda ke mun kaikai domin wata yarinyar in ka gan ta kamar ba Bahaushiya ba. Allah Ya shirya mana zuri’armu, amin.
Ikra Isah ’Yantakori, Katsina (08036141059): Hmm, kai dai bari FDK, lalle ka soso min inda yake min ƙaiƙayi. Saboda munin wannan ɗabi’ar da mafi yawan mata suka ɗauka a matsayin wai wayewa ya zarce tunanin mai tunani. Wayewa ko watsewa! Gaskiya yanzu nuna tsiraici da sunan kwalliya ta wayewa ya zama ruwan dare game duniya a tsakanin ’ya’ya mata, ba matan auren ba, ba ’yan matan ba, ba zawarawan ba; domin mafi akasari kowace idan za ta fita sai ta yi shiga ta fitsara ta yadda babu wani abu ɗaya jal na tsiraici da ba ya bayyana a jikinta. Mata ku san fa cewar nuna tsiraici ba shi ne kyawu ba, kyawu na nan ga yadda kika rufe jikinki. Allah kyauta.
Muhammad Yunusa Kasai (07066097012): FDK, ni ma wannan abun ya dade yana ci man tuwo a kwarya da fatan mata za ku dau izina daga wannan kunkurun. Allah Ya ba da ikon kiyayewa.
Gimbiya Asma’u-Kano (08034584157): Barkanmu da shan ruwa FDK. Tsiraici ga wasu kwalliya ce domin da ita suke ci, suke sha da biyan sauran bukatu har da na iyaye, domin za ka ga yarinya ta yi shigar banza, saurayi ya zo gidansu da mota ya dauke ta sun fita, iyaye na kallo ba su iya hanawa. Akwai matsala a wannan lamari, gaskiya.
Anisat Abdullahi Adamu Daura (07067716102): FDK, ina maka fatan alheri. A wannan zamani da wasu ’yan mata ke bayyana tsiraici da sunan kwalliya ko wayewa, ya zama abin Allah wadai. Don haka mata masu shigar nuna tsiraici ku dauki darasi daga kunkuru. A wani lokacin har da laifin iyaye don a gabansu suke sa wa. Sanya wadatattar sutura da za ta rufe maki duk jikinki shi ne garkuwa da mutunci a wurin mutane.
Ibrahim Albani Gombe (08084323239): FDK, ka yi gaskiya. Duk wadda ta ji kuma ta kyale sai ta yi nadama, domin wannan darasi ne ga kowa, mace da namiji. Mu dinga yi wa ’ya’yanmu, kannenmu, yayyenmu nasiha da shiga ta kamala.
Nazifi N.M.S. (09070950702): Salam haka ne! Ta yaya tsiraici zai zama kwalliya?
Y.Y. Dantsoho Kaduna (08079901259): FDK da sauran mabiya wannan fili, barkanmu da Sallah, da fatan Allah Ya karbi azumin da muka gabatar. Lalacewar Tarbiya da watsi da addini suka kai haddasa bayiyanar da tsiraici a fili. Hakazalika irin fina-finan Hausa da Turanci da ake kallo a yau sun kara gurbata al’umma, musamman mata. Daga gida gun iyaye abin ya fara baci, son ’ya’ya ya hana tsawatarwa. In wani ya nemi yin haka sai a ce, ji da naka ko kuma ‘sa ido ne.’ Ko wajen ankon biki, matsattsu ake dinkawa don jawo hankalin namiji. Abin ya fi kamari a manyan makarantun boko, inda wajen bikin bazday abin da ke faruwa ba kyan gani wajen mata.
Irin shigar da matan aure ke yi a matsayin Musulma, kai ka ce anya ba a kusa tashin kiyama ba kuwa? Gaskiyar magana, Shaidan na samun galaba. Allah dai Ya kare mu, in mun kiyaye.
B.K. Kaduna (08023783075): Ni kam in na ji mata na batun neman ’yancinsu, mamaki nake domin ga ’yan uwansu ko’ina suna yawo a tsiraice, musamman ’yan mata. Ina batun darajawa a nan, balle batun ’yanci? Su yaki wannan lamarin ya fi masu. Manzon Allah (saw) ya ce, bai bar wata fitina ba a bayan kasa face mata. Musulunci ya fada mana cewa, mace dukkanta tsiraici ce face fuskarta, ita ma din an ce ta suturta ta idan za ta fita ya fi. Mata kuna da babban kalubale tare da ku.
Ya’u Abban Amir (08064584107): Madugu uban tafiya FDK, ina maka fatan alheri. A zahirin gaskiya na fahimci wani abu, gaskiya mata suna da kalubale. Sun kware wajen wasa da damarsu. Duk macen da ke barin tsiraicinta awaje, wai don da namiji ya gani, ma’ana ita mai son abun duniya ce; to ka ga ba a Magana. Kamar saurayi mai neman mata, shi ma mazinaci ne. Allah Ya tsare mu.
Aminu Ibrahim Birnin Ruwa Gusau (08062790091): Gaskiya wannan zamani mata sun zubar da mutucinsu a banza amma ina musu fatar Allah Ya fahimtar da su bisa ga fadakarwarku, Allah sa haka, amin.
Dahiru Dauda (KGY) Bindawa (08055552897): Abin da na fahimta shi ne, hakikanin abin da yake wakana ne a cikin rayuwarmu ta yau, tsokacinka ya kawo. Ina fatan masu yi su fahimci cewa hakan ba wayewa ba ce, zubar da mutuncin kai da kai ne tare da tozarta gidajen da suka fito, duk da cewa su ma gidajen akwai kason nasu laifin a kan faruwar lamarin. Fatata ita ce duk a taru a gyara domin samun tsira.
Abdul Abdulhamid Zamfara (08167515363): Tabbas bai kamata a ce ’yan matan Hausawa Musulmi suna tsiraita jikinsu da sunan ado ko wayewa a wannan zamani ba, domin al’ada ce ta wata kabila daban. Amma duk da haka ba a taru aka zama ɗaya ba, don har yanzu akwai wadanda suka san darajar suturar jikinsu.