Batun yajin aikin ’yan sanda
Wadansu ’yan sanda da yawansu ya kai dubu 15 sun yi barazanar tafiya yajin aiki ko kuma su yi wa zabe mai zuwa kafar ungulu, sun yi wannan barazanar ce domin ta haka ne kawai za a biya musu bukatunsu. Wadannan ’yan sanda da suka yi wannan barazanar sun hada da masu mukamin Insifekta da […]
Wadansu ’yan sanda da yawansu ya kai dubu 15 sun yi barazanar tafiya yajin aiki ko kuma su yi wa zabe mai zuwa kafar ungulu, sun yi wannan barazanar ce domin ta haka ne kawai za a biya musu bukatunsu. Wadannan ’yan sanda da suka yi wannan barazanar sun hada da masu mukamin Insifekta da Mataimakin Sufurtanda wadanda aka yi wa karin girma a Disamba, 2013.
Wadannan ’yan sanda sun yi korafin cewa tun da aka yi musu karin girma ba a biya su alawus-alawus da kuma albashinsu na daidai da karin girman da aka yi musu ba. “An yi mana karin girma a watan Disamba, 2013, sannan a jikin takardar karin girman an bayyana za a fara biyanmu albashi daidai da karin girman da aka yi mana daga ranar da aka rubuta a jikin takardar.” Inji ’yan sandan. “Mun zauna zaman jiran tsammani na shekara daya (2014) don a biya mu, amma shiru kamar an aiki bawa garinsu, inda suka ce har yanzu ba a bayar da kudin ba. A watan Janairu (2015) an biya mu albashi daidai da karin girman da aka yi mana, amma ba su biya mu ariyas din wata 13 ba. A yanzu ga zabe ya karato, sun kuma ce kada mu goyi bayan kowa. Ta yaya za mu yi haka bayan an danne mana hakkokinmu?”
Amma mai magana da yawun ’yan sanda, Mista Emmanuel Ojukwu ya shashantar da batun barazanar yajin aikin da ’yan sandan suka yi, inda ya bayyana “wannan wani aiki ne na bata-gari da suke so su kawo matsala a zabe mai zuwa. Ba mu yi barazanar shiga yajin aiki ba, kuma duk dan sanda da ya yi haka zai fuskanci fushin doka, za a kuma hukunta shi don ya zama izna ga ’yan baya.”
A yanzu da hukumar ’yan sanda ke nuna wa jama’a komai na tafiya daidai, ya kuma zama dole su yi bincike a kan matsalolin da suka shafi wadannan ’yan sanda da aka yi musu karin girma, musamman ma idan aka yi la’akari da halin da kasar nan take ciki, inda nan da ’yan kwanaki za a fara gudanar da zabe. Ana sa ran ’yan sanda za su taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ingantaccen zabe da ba ya dauke da tashin hankali. Don haka a tabbata an magance duk wata baraka da za ta iya haifar da barazanar tafiya yajin aikin.
Kodayake ba wannan ne lokaci na farko da ’yan sanda suka yi yunkurin tafiya yajin aiki ba, ko a shekarar 2002 wadansu ’yan sanda sun yi barazanar tafiya yajin aiki saboda rashin biyansu hakkokinsu, a lokacin hukumomin ’yan sandan ba su dauki hakan da gaske ba har sai da ’yan sandan suka kaurace wa wuraren aikinsu, inda hakan ya haifar da dimbin matsaloli a lokacin. Gwamnati ta kira matakin da ’yan sandan suka dauka a matsayin cin amanar kasa, sannan ta umarci sojoji su je wurare masu muhimmanci da ake tsammanin komai zai iya faruwa saboda kauracewar ’yan sanda, sannan ta yi yunkurin kora da hukunta ’yan sandan da suka je yajin aikin.
Ba karamar illa za a samu ba idan har aka bari ’yan sandan suka tafi yajin aiki ba tare da an yi wa tufkar hanci ba. Kwata-kwata bai dace a bari jami’an tsaro su rika furta batun yajin aiki ba, halin da ake ciki a yanzu ya bambanta da wanda aka shiga a shekarar 2002. Babu wani dalili da ’yan sanda za su rike a matsayin hujjar da za ta sanya su kaure wa wuraren da aka tura su aiki ba, ya kuma zama dole hukumomi su tabbatar da hakan. Duk da cewa za a iya cewa wadannan ’yan sanda suna da kwakkwaran dalili na barazanar tafiya yajin aiki, ya kamata a duba wannan batu sosai, su kuma wadannan ’yan sanda ya kamata su sani ya zama dole su yi hakuri, domin abin da hakuri bai bayar ba, rashinsa ma ba zai bayar ba, domin idan suka tafi yajin aiki komai zai jirkice a kasar nan. Unifom din da suka sanya ya zama dole su kasance masu kishin kasa. Za su iya amfani da batun zabe don hukumominsu su saurare su, amma ba wannan ne lokacin da za su furta batun tafiya yajin aiki ba. Yin hakan zai bakanta kasar nan a idon duniya.
A yanzu dai ya zama dole ’yan sanda su tashi tsaye wajen yin aiki tukuru don kare kasar nan, sannan ya zama dole hukumomin ’yan sanda su yi abin da ya dace don dakatar da batun yajin aikin da wadansu ’yan sanda suka yi barazanar tafiya.