Batun Yunusa da Ese: Za mu tabbatar an yi adalci – dahiru KT
Alhaji dahiru KT, shi ne shugaban kungiyar ’yan Arewa mazauna Jihar Bayelsa. A tattaunawarsa da Aminiya ta waya, ya bayyana cewa wasu tsiraru ne suka haddasa matsala cikin al’amarin, da an warware shi cikin sauki tun da farko. Aminiya: Ko za ka yi mana karin bayani abin da ka sani game da wannan al’amari na […]

Alhaji dahiru KT, shi ne shugaban kungiyar ’yan Arewa mazauna Jihar Bayelsa. A tattaunawarsa da Aminiya ta waya, ya bayyana cewa wasu tsiraru ne suka haddasa matsala cikin al’amarin, da an warware shi cikin sauki tun da farko.
Aminiya: Ko za ka yi mana karin bayani abin da ka sani game da wannan al’amari na Yunusa Yello da yarinya Ese?
Wannan magana dangane da Yunusa Yellow da yarinya Ese fa sarka-sarka ce, domin tun farko fa shi yaron nan a gidan su Ese yake, tun lokacin yana tuka babur Okada, har aka zo aka koma Keke Napep, nan gidansu yake zaune sama da shekara biyar zuwa shida. Ka san ita Ese, mamarta tana sayar da abinci ne, unguwar akwai Hausawa da yawa kuma suna sayen abinci a wurinta sosai. Kan haka Yunusa ya hadu da Ese kuma suka fara soyayya da juna kuma har ya kai su ga wannan yanayi. Inda daga bisani har suka shiga Kano tare, ba tare da sanin iyayenta ba. Amma abin da na sani shi ne, ita yarinyar ta nemi izini daga mamarta, cewa za ta kai wa abokinta ziyara, tana nufin Yunusa, amma ita mamar tata ba ta tambaye ta inda za ta ba kai tsaye. Sai bayan kwana daya zuwa biyu sai ta samu labarin cewa Ese tana Kano, don haka ta bi ta har zuwa can Kano din.
Aminiya: Kamar yadda muka samu tabbaci, a halin yanzu shi Yunusa yana hannun ’yan sanda a nan Jihar Bayelsa, ko ka san halin da yake ciki a matsayinka na Shugaban ’yan Arewa mazauna Bayelsa?
A yanzu dai ni ban sani ba, saboda ka san fa ita wannan maganar, na bi ta har zuwa Kano domin a samu maslaha, domin kuwa muna zaman lafiya da al’ummar Bayelsa. Babu inda muke zaune lafiya kamar nan, domin su ’yan Bayelsa sun dauke mu kamar uwa-daya-uba-daya ne, ana yo tabargaza ba su nunawa ko su nuna damuwarsu, za su shanye. Sun dauki Bahaushe dan Arewa kamar dan uwansu, ba su da wani wulakanci ga Bahaushe da ke zaune nan Bayelsa.
Aminiya: A kungiyance, ku ’yan Arewa, wace rawa kuke takawa kan batunsa, domin ganin ba a wuce makadi da rawa ba wajen daukar mataki kan shi Yunusa Yello?
Wannan al’amari fa, wani abu ne da babu wanda ya fi karfin jami’an tsaro ko kuma hukuma, babu wanda ya fi karfin gwamnati. Muna dai son duk abin da gwamnati za ta yi, ta duba, domin shi dai wannan al’amari, soyayya ce. Kuma ka san ita soyayya ciwo ce, amma kuma ka san ita wannan yarinya ana kuka cewa shekarunta ba su kai ba, wanda za a ce ta bi shi Kano ba tare da matsala ba. Wannan shi ya kawo duk wannan matsalar, amma shi yanzu abin da muka sani, magana dai na hannun hukuma, ita ce ke yin bincike kan al’amarin, ita ce ta san abin da za ta yi a kan al’amarin Yunusa. Idan akwai abin da za a yi a fitar da shi, ko kuma yarinyar, wacce ita ce ke sonsa, domin ta ce idan ba tare da shi ba, ba za ta iya rayuwa ba ko, kuma idan iyayen sun ga cewa za su bar wa Allah, to mu dai muna nan. Yanzu dai mun samu kwanciyar hankali, domin yarinyar nan al’amarinta ya tada mana hankali a nan Bayelsa. Wannan tashin hankali kuma, gaskiya har ga Allah har da ’yan uwanmu ’yan Arewa. Domin tun da farko da muka je Kano da mahaifiyarta, da sun amince sun ba mu wannan yarinya mun dawo da ita, da duk wannan al’amari bai faru ba. Saboda babu wani da zai so ya ji cewa an zagi ubansa a nan, to kamar yadda nan Bayelsa suke maganar cewa yarinya tana gidan sarkin Kano, wai an boye ta, ni ne nan na fito na kareyata batun nan. Na ce masu yarinya ba ta hannun sarki Sanusi, ba su da wata alaka, domin shi ne ma ya ba da umurnin cewa a mayar da ita ga iyayenta. Don haka, ’yan hana ruwa gudu ne duk suka haddasa wannan al’amari.
Aminiya: To wane mataki kuke dauka a kungiyance domin kawo maslaha a maganar Yunusa Yellow?
Ka san fa maganar nan ta yi zafi sosai a Bayelsa, idan gwamnati ta yi bincike tana ganin akwai wani abu da za mu iya yi, dole za ta neme mu. Idan mun ga abin da za mu iya yi kan batun, domin ganin cewa an sasanta maganar, to za mu yi. Idan kuma gwamnati ta ga cewa abin da yaron nan ya yi bai dace ba, dole ne a hukunta shi, da ma mu ’yan gwamnati ne, wannan al’amari kuma, dole ne gwamnati za ta duba ta dauki matakin da ya fi dacewa. Idan gwamnati ta ga cewa akwai wata rawa da za mu taka, idan batun sulhu ne, ta neme mu ko kuma cewa sun yarda Yunusa zai auri yarinyar nan, saboda mun ji wai an ce tana da ciki wata biyar, mu dai mun bar wa Allah al’amarin nan, domin babu abin da ya fi karfin Allah.
Muna yin iya bakin kokarinmu mu ga an yi wa Yunusa dahiru adalci a shari’ar da ake yi masa ta hanyar tuntuba tare da ganawa da lauyoyin da ke rike da shari’ar, duk da cewa ya zuwa ranar laraba bayan an kai shi kotu an mayar da shi gidan wakafi, kafin ranar litinin 14 ga watan nan domin ci gaba da shari’ar.Mun zauna da lauyoyinsa sun ce mana maganar Yunusa magana ce da suke bi, kuma ka san lamarin soyayya yadda take ciwo ce, idan Allah Ya hada mutum da mutum, suka ce za su tabbata an yi masa adalci. Kuma ranar litinin din ne ake sa ran ita mahaifiyar Ese da Yunusa duk za su bayyana gaban kotu domin bayar da bayanansu.
Aminiya: Ko akwai auratayya a tsakanin ‘yan asalin jihar Bayelsa da ’yan Arewa mazauna jihar?
Ai wannan batun yanzu auratayya take wakana a tsakaninmu da ’yan asalin Bayelsa, domin ni shaida ne, na halarci daurin aure irin wannan a karamar hukumar Kolokoma/Okpokuma, yarinyar ma a Zariya aka goya ta, aka yi bikin a Kaduna, yanzu haka ma tana Jaji tare da mijinta, wanda a karshe nine ma na zama uban yaron da ya aure ta. Ai da yawanmu hausawa akwai wadanda suka auri ’yan asalin Bayelsa suke zaune tare da su har yanzu.