Baturen dalibi

Wani dalibi ne ya je makaranta a makare, da ya isa ajinsu sai ya iske malamin Ingilishi ne ke ciki yana koyarwa. A ka’idarsa, ya ce idan yana aji duk wanda zai yi magana sai dai ya yi da Turanci, idan ya yi da wani yare za a hukunta shi. Malamin sai ya tambaye shi […]

Baturen dalibi
Baturen dalibi

Wani dalibi ne ya je makaranta a makare, da ya isa ajinsu sai ya iske malamin Ingilishi ne ke ciki yana koyarwa. A ka’idarsa, ya ce idan yana aji duk wanda zai yi magana sai dai ya yi da Turanci, idan ya yi da wani yare za a hukunta shi. Malamin sai ya tambaye shi da Turanci: “What is your name?” (Yaya sunanka). Sunansa na ainahi Sabo Sule, don haka sai ya amsa da Turanci ya ce: “My name is New Ten Kobo.” Malamin ya sake tambayarsa: “From where are you?” (Daga ina kake)? Daga karamar Hukumar Kura yake, sai ya amsa da Turanci cewa: “I’m from Hyna Local gobernment.
Daga Khalil Muhammad, 08031908918