Baturen Hauhawar Hawan-sa (2)
Haurobiyawa na da masaniya kan yadda Baturen Hauhawar Hawan-sa ya gina katafariyar Farfajiyar koyon watsattsaken tawada da alkalami, tare da falle holamar shafukan wagagen littattafai cikin shekarar alif sili da manuniyar kasa da kwanciyar magirbi, a birnin Dabo inda ba dabo, inda dimbin al’umma suka yi koyi ka koyar kwabo da kwabo, ba tare da […]
Haurobiyawa na da masaniya kan yadda Baturen Hauhawar Hawan-sa ya gina katafariyar Farfajiyar koyon watsattsaken tawada da alkalami, tare da falle holamar shafukan wagagen littattafai cikin shekarar alif sili da manuniyar kasa da kwanciyar magirbi, a birnin Dabo inda ba dabo, inda dimbin al’umma suka yi koyi ka koyar kwabo da kwabo, ba tare da kwambo da bobon bokoko ba. Halin yau kuwa mun fasko yadda ake tsuwurwurta KOYI KA KAUTAR; KWASHI KA KARKATAR da sauran miyagun ta’adun da ake yi wa al’umma dundun danniya da handama da babakere.
Batu na ingarman karfen karafan titin taragon layin kwangirin dogo, ba tare da bata lokacin wulwulawar agogo ba, a daukacin kasashen da Turawan mulkin mulaka’u suka yi mulki sun horar da al’ummar kasashen ne yadda ake bin turbar tafarkin tsarin rayuwarsu don takun tattakin ninkayar iyo da fito a kogin zamani. Maimakon al’umma su koyi takun zamanin sai suka karke da tata-tata al’amarin da ya haifar musu da koma-baya. Kai akwai wani masani mai watsattsake, WALWALIN-TANTANIN RUdANI, wanda ya yi wa wagegen kundinsa taken ‘YADDA TURAWAN TURAI SUKA TAKURE IFRIkIYYA,’ a halin yanzu kamata ya yi a sauya taken kundin ya zamo YADDA TUKURURU YA TUNKUdA IFRIkIYYA CIKIN RUKWATUbO
kiren karyar karairayi suka dabarbarta tsarin koyi ka koyar, musamman a tsarin zamaninmu na BOBO DA kWAMBON BOKOKO. Lallai mu himmatu ka’in da na’in wajen ganin masu laluben NA-KOKO ba su yi mana karfa-karfan kOTON kATO DA kATO ba. Domin miyagun ta’adun da MAGABTAN MAGBATA, wadanda ke ikirarin kwarewa a fannonin ilimi ke tsuwurwurtawa suke yada JUHALA, su BADDALA ADALA, har al’umma ta karke da LALALA!
Mutanen da ke cikin WAHALA an ki kyale su su sakata su WALA, inda aka bar ’yan WALA-WALA, suna ta cin ALALA, amma gama-garin al’umma an hada su da GAJALA. Kuma bayan sun dundume kururu a tsala musu BULALA, har jikinsu ya yi lilis su yi ta fama da KASALA. Lallai wajibi ne hukuma ta lalubo bakin zaren kULLA-kULLA, don share wa al’umma kWALLA, ta yadda za a fice daga MATSALA.
Baban-burin-huriyya a tabbatar an yi wa Fullo kurtun halo alalo, yadda zai sake sabon salon kiwon bisashe a makekiyar makiyayar fullo, kwatankwacin irin ta DANNIYAR-MAKI, ko mun huta da make-maken kiren kairairayin masu bobo da kwambon bokoko da ke yunkurin ganin lallai an yi sako-sako wajen kula da nagge da karsana da bijimi, an bar masu dakile ci gaban Arewatawa na ta hantarar al’umma, alhalin Turawan Turai na kiwon bisashe, kai kusan ko’ina a mafi yawan kasashe.
Lallai lokaci ya yi da masana za su dubi shafukan litattafan da aka jibge tsibi-tsibi a rumbun ilimin Baturen Hauhawar Hawan-sa, wanda ya yi aiki tukuru ba wasa, wajen yaki da juhala. Duk da cewa manufar Malam Bature ta samar da ’yan kwadago ga Turawan mulkin mulaka’u ce, ai ya kamata a ce mun sabunta salo, mun solle jibar da aka jibga mana da soso da sabulun salo.
Kuma daukacin masana kundin labaran da, da na yanzu, da masu fahimtar dabi’ar dan Adam sun fasko cewa farare sun fifita a kan bakake ne, ta hanyar fafutikar famfarar farare, yayin da bakake ke ta bugun burgar bagire. Don haka a mafi yawan lokuta a kan karke da barambarama da barusa. Shi ke nan Turawan Turai sun ture kowa-da-kowa, ’yan Ifrikiyya kuwa sun karke da turereniya.
Bisa la’akari da al’amuran da ake tsuwurwurtawa a sararin duniya, lallai mu daina mamakin gani ko jin: Tattalin tunkahon Turawa; Lungunan Logar Luggar Larabcin Larabawa; Sasarin Siriyawa; Yamutsin Yamanawa; Janjimin jami’an Japanawa; Jarumtar jaruman Jamusawa; Farin cikin Faransawa; Birgimar burgar bunkasar Birtaniyawa; Rugugin raka-rakar rarakar rokar Rashawa; Sauyin salon sansanin Sinawa; Turakun tarairayar ’ya’ya da uwa a turka-turkar Tukawa; Amarar ajon Amurkawa da dai makamantansu.
Sannan a bangaren Ifrikiyya, musamman a dundumin da’irar Haurobiyawa mun sha ji da ganin yadda ake: Azancin Auzinawa; Artabun Arewatawa; Barankadamar baragurbin buga-bugar Ba’are; Carin carar cakwaikwaiwar cancarewa, al’amarin da kan sa a karke da haushin haramben harigidon Haurobiyawa, masu rawar yanyanwa ’yan yawa! Kantakaryar kantoman kuratan kare yawa!
Lamarin dai da ya fi jikkata Arewatawa tare da daukacin Haurobiyawa, shi ne yadda aka kasa yi wa Babban mutum mai rawani tanadi a kundin mulkin kasa, musamman in an yi la’akari da yadda Turawan mulkin mallaka suka ja ragamar al’umma ta bayan fage, wato ta hanyar bayar da umarni ga masu rike da mukaman gargajiya, wajen tarairayar harkokin rayuwa. Yau kuwa, masu rike da wadancan mukaman sun zama na zamanin da, ko ma a ce GARGAJIYA, wadda ta rikide ta zama GARARAR-GAJIYAR-JIYA. A dai waiwaya baya a duba gagarumar gudunmawar da suka bayar a da, domin daidaita tattakin-takun-tafiyarsu a doron balaguron zamani.
Haurobiyawa kada mu bayar da kafa ga masu watangaririya da kwakwalwar talakawa su ci gaba da dukan ta-molar Samson-siya-siya da hankalinmu. Lokaci ya yi da za mu yi fafutikar cin gajiyar fannonin ilimi da ’yan kasa suka kware a kai, ta yadda ba za mu kware ba, har magabtanmu su yi mana kwashi-kwaraf, inda da sun yi mana wa-ka-ci-ka-tashi, sun wawushe komai kakaf, bayan sun yi wa lalita karkaf, sai kawai su samfe da zarar sun samu kafar aron faden kolo su rare!