Baturiya ’yar shekara 62 ta yi saukar Al-Kur’ani bayan ta musulunta a Kano

Liliana Mohammed, ’yar kasar Bulgari mai shekaru 62, ta yi walimar saukar Al-Kur’ani a Kano bayan shekara 10 da musuluntarta.

Baturiya ’yar shekara 62 ta yi saukar Al-Kur’ani bayan ta musulunta a Kano

Liliana Mohammed, baturiya, ‘yar kasar Bulgari mai shekaru 62, ta yi saukar Al-Kur’ani a Kano bayan shekara 10 da musuluntarta.

Wata baturiya mai shekaru 62 ta yi saukar Al-Kur’ani daga wata mkarantar Islamiyya a Jihar Kano.

Baturiyar, ’yar kasar Bulagaria, mai suna Liliana Mohammed, ta yi saukar Al-Kur’anin ne bayan shekara 10 da ta musulunta.

An gudanar da walimar saukar Al-Kura’ninta ne tare da wasu dalibai uku a Makarantar Mamba’irrahman da ke Kano a karshen mako.

Malama Liliana ta ce tun daga lokacin ta Musulunta ta dukufa neman ilimin addinin Musulunci, kuma Musulunci ya kawo mata farin ciki da natsuwa a rayuwarta.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa Lilian ta fara zuwa Kano ne bayan aurensu da wani bahaushe dan kasuwa, Marigayi Alhaji Ibrahim Sambo, wanda Allah Ya azurta  su da ‘ya’ya biyu.

Yadda ta fara koyon karatun Al-Kur’ani

Malama Liliana ta bayyana cewa ilimin Al-Kur’ani da ta samu ya zame mata shiriya, kuma “Tun da na karbi Musulunci na samu kwanciyar hankali.

Ta bayyana cewa da farko ta fara koyon karatun ne a gida, saboda yawan shekarunta.

“Na fara koyon karatu ne a gida, inda Malama Hafsa take zuwa tana koyar da ni, muka faro tun daga karatun bakaken larabci.

“Haka ta yi ta koya mini, har na fara iya hada baki, ta kai ga na fara karatun Al-Kur’ani, har muka kai lokacin da nake biyawa da kaina.

“Tun ana yi min karin aya-aya, har muka fara kammala sura, har ga shi yanzu na yi sauka

Musulunci ya kawo min natsuwa

“Musulunci ya kawo mini aminci. Al-Kura’ni ya zame mini haske — duk lokacin da na karanta shi nakan samu natuwa da kwanciyar hankali,”in ji Malama Liliana.

Ta kara da cewa duk da yawan shekarunta, ta fara haddar Al-Kur’ani.

Ta ce tana jin dadin rauywa a Kano saboda yawan Muslumi da kuma sauki Kano wajen gudanar da addinin Musulunci.

Malama Liliana ta ce wani abin ban sha’awa da Kano shi ne lokutan ibada irin su azumi da na Sallah a nan ba su da sarkakiya kamar wasu wura.

Daya daga cikin ’ya’yanta mai suna Hamida Sambo, ta yaba wa mahaifiyar tasu bisa kyakkyawar tarbiyyar da ta ba su tun kafin ta Musulunta.

“Tun kafin ta Musulunta ta ba mu tarbiyya ta gari, da muka zama mutanen kirki a cikin al’umma.

“A matsyinta na Baturiya da ke zaune a Kano, ba ta hana mu mu’amala a dangin mahaifinmu ko yin addini. Muna mata addu’ar Allah Ya saka mata da Aljanna Firdausi,” in ji Hamida.

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa